LABARAI/NEWS

TSARUKAN TAZARAR IYALI, DA ABUBUWAN DA YA KAMATA A SANI

TSARUKAN TAZARAR IYALI, DA ABUBUWAN DA YA KAMATA A SANI

Bada tazara tsakanin haihuwa hanyace dakan taimaka wajen ganin Mata sun sami isashshen hutu kafin qara daukar ciki na gaba walau sanadiyyar wata larura ko sakamakon wani dalili na daban.

Akwai tarin hanyoyi kala-kala:

1-■ Akwai hanyar da ake kira “Natural” itace ta hanyar jinkirtawa namiji ya zare gabansa daga jikin mace yai abunda ake kira azalu… tana da inganci kaso 90% cikin dari na kaucewa samun ciki

2-■ Akwai ta hanyar shayarwa wato “physiologic” sakamakon bayan haihuwa mace na shayawarwa hakan kan jinkirta qara shigar ciki ga wasu saboda a lokacin sinadarin da ake kira “furolaktin” yayi HIGH, yayin da sinadarin “Gwanadoturofin” ke yin LOW wanda wannan rashin daidaiton tsakanin sinadarai biyun bazai bari ciki ya samu ba.

Toh saide wannan hanyar na bukatar wasu abubuwa kafin tai aiki da kyau: Ya danganta da yawan shayarwa, tsayin lokacin da ake shafewa ana shayarwa, lokacin da aka somo irin wannan shayarwa ya zamto tun bayan haihuwa ne, yanayin koshi da lafiyar ita kanta mai shayarwar…. da kuma irin shayarwar wato nono ne zallah tsawon watanni shida ko kuwa ana hadawa da baiwa yaro ruwa…. wannan yasa bakowacce mace ke ganin tasirin hanyar ba.

3-■ Akwai “Hormonal method” ta hanyar amfani da Magungunan Sha’ (Oral Medication)

Ita wannan hanya ta shan magani kullum-kullum wasu dada mahimmancinta shine; Yakan hana mace fuskantar matsanancin ciwon mara yayin haila, tana kare mace daga hatsarin karancin jini (anemia), tana kare mace daga cuttukan nono wato “benign breast dx” ba cutuka masu alaka da kansar nono ba – babu bayanin da ya nuna hanyar na bada kariya daga breast cancer, tana taimakawa mace wajen ganin haila kowanne wato akai akai, tana ragewa mace hatsarin kamuwa da cutar PID, tana kuma ba mace kariya daga hatsarin kamuwa da kansar babban hanji wato (colon cancer)

Saide kuma hanyar na karawa matan dake dauke da ciwon kai na gado na 6arin kai daya wato (Migraine) hatsarin fuskantar shanyewar wani sashi na jikinsu wato STROKE kwarai da gaske, Ba aba mace mai Migraine za6i kan wannan hanya, haka in son samu kar aba masu hawan jini ko ciwon suga za6inta suma, Sannan tana karawa mace hatsarin kamuwa kansar bakin mahaifa (cervical ca) musamman in akwai ciwon ga wani na kusa da ita cikin yan uwa da kuma yiwuwar caccanzawar halaye; ya zamto haka kurum kaga mace ta hau 6acin rai, ko abunda ya bayyana afuskarta daban amma abunda take fadi daban.

Sai mahimmin abu; Idan mace na amfani da wannan hanya to akwai magungunan da ya dace tasani amfani dasu na rage ingancin maganin koma azo karshe a6ishe da samun ciki; domin magungunan da mace ke sha na hana hormonal din aiki, kuma ko ke jami’ar lafiya kafin ki rubuta magani ya kamata ka tambayi mace tana planning ko a’ah

Wadannan magunguna sun hada da rukunin Antifungal wato (Fluconazole, ketoconazole,) Anti T.B wato da akan ba masu tarin fuka su (Rifampin) ko Antibiotics wato su ja da yelo da amfisilin (tetracycline & Ampicillin) wadannan magungunan na hana Oral contraceptive aiki… don haka inkina da infection aka baki fluconazole ki fadawa likita kina shan OCP’s

Saide kuma magunguna irinsu VITAMIN C da Paracetamol na qarawa OCP’s din karfin aiki.

Akarsh de musani duk hakan bai nuna duk wanda yai amfani da hanyar oral zai fuskanci wadancan side effects din da nai bayani, A’ah idan har ya kar6i jiki toh shikenan.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

4-■ Akwai “Hormonal Method” ta hanayar Allura “Injectable”

Wannan ita bata bukatar maganin sha kullum galibi allurace idan akai sau 1 toh sai kuma bayan sati 12 ko watanni 3 kafin aqara yi.

Toh saide wannan hanyar ta allura na iya sa mace ta fuskanci side effects; wanda suka hada da Rikicewar kwanakin al’ada, ganin jini tsakanin periods (spotting), Sannan ga wadanda suka dade suna amfani da hanyar bayan dakatarwa kaso 70% kan fuskanci jinkiri kafin cikin ya samu, wasu ko sun dakatar musamman in sun dau tsawon lokaci suna yi akwai yiwuwar sai sun jira shekara 1 ko 2 kafin aga ciki ya samu…

Amma kuma wannan hanayar nada wasu kariya:
Bata haddasa zagwanyewar 6argo (osteoporosis) kamar yadda wasu kan alakantata dashi, Bata haddasa hatsarin saurin karyewa, bata sa yanayin kitse ajika ya qaru… saide ma HDL cholesterol wato Good cholesterol ya qaru wanda ke baiwa zuciya kariya, bata kusanta mutum da hatsarin fuskantar bugun zuciya, Saide tana dansa adadin sugar acikin jinin mutum ta qaru amma ba yadda zata kai ga matsala ba… Amma in mutum nada ciwon sugar to anan ne sai anduba yanayin control din sugar ajikinsa kafin abashi za6inta saboda gujewa side effects din, tana iya sa aga nauyi ko kiba ta karu akalla 1kg zuwa 2kg, Masu shayarwa ma ana iya yi musu ita ba matsala, tana rage hatsarin kamuwa da karancin jini, PID da kuma kare mace daga hatsarin ciwon cancer.

Sannan hanyar amfani da allura bata da alaka ta kusa ko nesa da ciwon kansar bakin mahaifa (cervical cancer), ko kansar nono (Breast cancer)

5-■ Sai hanyar “Subdermal Implants” wato rods da akansa acinyar hannu, shima kala kala ne, amma ba wannan bayanin xan ba,

ita wannan hanya idan akasa rods din tana iya shekara 3 zuwa 4 tana aiki, saide in lokacin ciresa yayi aje a canza, ana iya kuka ciresa ako yaushe aka so… Yadda yake aiki shine hanyar nasa majinar bakin mahaifa tai kauri zuwa cikin mahaifa yadda ko mace tai ovulation kwan bazai zauna ba cikin mahaifa santsi zai jawo kwan yayo waje.

Saide tana da side effects dinta hanyar wanda ya hada da; Sanayar cikin mahaifar mace ya motse ko ya rasa kaurinsa, rikicewar haila, ganin jini tsakanin haila ko ta rika qara kwanakinta, sannan ansamu wasu kan korafin tana sasu yawan fuskantar pimples a fuska, ciwon kai, ko kiba. Musamman tsakanin mata bakaken fata namu na Africa anfahimci impanon nasasu nauyi ko kiba.. toh saide ba wata kiba bace can da za’a damu.

Saide kuma wannan hanyar nada wani mahimmanci wajen; Rage kitse ajika domin kare mace daga hatsarin stroke, ko ciwon zuciya da magudanan jini, bata shafar sugar ajikin mutum ko yadda jikin ke sarrafa sugar, bata shafar kwarin ķashin mutum, ba matsala don ana shayarwa… Sannan haihuwa na dawowa nan da nan da zarar ancire.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

6-■ Akwai “Barrier Method” wanda a karkashin wannan ne akwai abubuwa irinsu:

▪︎Amfani da Latex rubber condom: Wanda namiji zaisa roba agabansa saboda koda maniyyi ya kuccemasa zai zamto yana nan de cikin robar bazai shiga jikin mace ba, akalla tana bana kariya 98%, wannan hanya kuma na bada kariya daga kamuwa da cuttukan saduwa daka iya yaduwa kamar su Herpes, Hepatitis B, Syphilis ko HIV da sauransu

▪︎ Akwai Vaginal spermicide: wato maganin ana matsa shi ne cikin farji kafin jima’i ta yadda hakan xai hana maniyyi shiga cikin mahaifa tare da rage masa quality ta yadda saide ya kwaranyo ya fito.

Shima yana bada kariya daga cuttukan da aka iya dauka ta hanyar saduwa, da infection na vaginosis…

▪︎ Akwai “Vaginal barrier” ta hanyar amfani da abunda ake kira diaphragm da Cervical caps: Shi suna rufe bakin mahaifa yadda ko maniyyi ya kucce basai sami kofar shiga mahaifa ba. Suma suna bada kariya daga cuttukan da aka iya dauka ta hanyar saduwa, kansa da kuma ciki awajen mahaifa. Saide akwai hatsarin haddasa infection a mafitsara.

7-■ Akwai “Intrauterine Device (IUD)”
wanda ake saka implanon din acikin mahaifar mace ta yadda zaike sakin fibrin da phagocytic cells da zasu hadiye kwan mace koda tai ovulation ta yadda ciki bazai samu damar shiga ba.

IUD musamman ya kasu kashi biyu… Hormonal IUDs (Liletta, Kyleena, Mirena, and Skyla) wanda yake sa period ya zamto light ba jini sosai kuma atakaitattun kwanaki sai kuma Copper IUD (ParaGard) wanda ashi anfi ganin mata na fidda jini mai yawa yayin haila… Amma de dukkansu inta juya ana ma iya dena ganin hailar…

Wannan hanya na bada kariya daga samun cikin a wajen mahaifa (ectopic pregnancy) sannan tana saisaita yawan jinin da mace kan fitar yayin haila ta rage yawansa….

Hatsarin ectopic pregnancy dalilin wannan hanya kurum a watannin 4 na farkon sashi ne shikenan. Sannan kuma inde mace na kula da tsafta ba zance infection.

Nan da nan haihuwa ke dawowa da ancire, ana masa laqabi da Excellent Contraception.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

  1. Akwai “Billing Method”

Wacce wasu kan kira da calender wacce wannan nasha bayaninta basaina tsawaita ba. Akan tsallake wasu kwanaki ne guda 5 zuwa 6 da ake tsammanin mace zatai ovukation sai a kaurace ma saduwa, Galibi de daga kwana 7 bayan gama haila.ga masu yin haila duk bayan kwana 21, da kuma.daga kwana 11 bayan gama haila a masu yin haila duk bayan kwana 28,

Itama lafiyayyar hanya ce bata da hatsarin komi

  1. Sai hanya ta karshe wato “Sterilization” wannan hanyar planning ce ta dun-dun-din da ake ga wadanda sukejin su sun kammala haihuwa… hanaya ce da ake katse bututun dake sauko maniyyi a namiji, ko kuma gutsure bututun follopian tube din mace wadanda saidasu ne kwan mace zai iya biyowa ya shiga mahaifa.

☆☆▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎▪︎☆☆

Bayin Allah masu karatu wadannan sune hanyoyin planning da muke dasu, kowacce kuma kunji abunda take kunshe dashe, baka rasa hanyar planning da saide effects, amma bakowa bane ke fuskantar hakan saide in anga hakanntoh kar a tsorata, ansan abune da dama anatsammaci ganin hakan.

Galibi wasu kan dau side effects su rika bayaninsa amatsayin illolin planning, wannan ba daidai bane. Abunda ake kira illa shine Complications amma ba side effects ba. Saboda haka duk hanyar data kar6i mace itace daidai da ita. Ba dole sai kowa yai iri daya ba.

☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆☆

SHIN A LIKITANCE WACCE HANYA CE DAIDE NI ???

Manyan likitoci da kuma medical Journals of Reproductive health sun fitar da wasu shawarwari kamar haka:

🎍
1- Macen dake da ciwon ta6uwar kwakwalwa wato (psychiatric illness) dakan taso lokaci lokaci kumq suke galibi har iya tsawon rayuwa ahaka; toh ana iya bada za6in dorata akan: Oral contaceptive nasha, Sanya mata implanon, Allura (DMPA), IUD ko amfani da Barrier Method.

🎍
2- Macen da intai rauni jikinta jini baya tsayawa akan kari wato coagulation disorder: Za6inta shine Oral contraceptive na sha

🎍
3- Macen dake da larurar ciwon kafafu da jini ke gudaji ajikinta wato Thrombosis: Aguji bata maganin Contraceptive dake kunshe da Iyistrogin…. sai hanyar dake da projestrone kurum

🎍
4-Wacce take da KIBA ko kitse da yawa ajiki, High cholestrol: Abata lowa dose na oral contraceptive bayan anyi control din kitsen, idan har TRIGLYCERIDES din mace yai HIGH to aguji bata maganin tazara na sha wato Oral. Abata Progestin only pills nasha, ko progestin na allura, ko IUD progestin banda estrogen shine acceptable abunda aka yadda don gudun stroke.

🎍
5- Mace mai farfadiya ko jijjiga (Epilepsy ko seizure): Galibi maganin da ake basu domin ciwon su yana rage ingancin Maganin planning na sha wato OCP’s da kuma ingancin Implants… shyasa wasu duk da ga planning din aka ganinsu da ciki karshe.

Don haka irin wadannan mata masu Epilepsy ana iya basu Oral contraceptive amma wanda ke kunshe 50microgram na Estrogen, ko ai musu amfani da Allura DMPA, ko IUD’s na sawa acikin mahaifa… shine daidai dasu.

🎍
6- A Mata masu hawan jini kuma masu matasan shekaru (young women) wanda ba wasu risk factors din iya hawan jini ne kuma jinin anyi control dinsa da kyau baya hawa; A iya bata low dose na Progestin OCP’s ko Allura DMPA, Implants, ko IUD, sune akafiso.

🎍
7- A Matan da suka ba 40 baya kuma suke da Hawan jini, kila suke shan taba, kuma hawan jini bawani control me kyau… toh duk ana iya musu amfani da sauran hanyoyin planning amma banda maganin sha ta baki wato OCP’s

🎍
8- Masu ciwon suga: Progestin only Ocp’s, Implants, IUD’s ko har Allura idan sugar din anyi control dinta da kyau.

🎍

  1. Masu fama da ciwon kai irin Migraine: Ai musu amfani da Implants ko Allura DMPA….

🎍

  1. Macen data haihu: Bayan sati 4 da haihuwa tana iya fara planning, musamman progestin only mini pills, inko implants nema ko yaushe ana iya sawa.

💐💐💐
Wannan shine abunda ya kamata asani. Su ragowar hanyoyin kamar su Billing methods, condom, natural methods, barrier methods wadannan su kowa zai iyayi shyasa ban maganarsu ba.

Sai kuma ku nemi daya post din yana nan asaman wannan a timeline dina domin jin bayani akan abunyi in ana ganin jini, ko periods na wasa ko kuwa ma ciki ya samu alhalin ana planning… Alhamdulillah ☘ Fatan an ilmantu

Don Allah masu copy & paste koda zaku cire suna nan ban yadda ayanken wani parts na rubutuna ba, duk kuma wanda yai hakan hankalina yakai kansa toh kar yai mamakin abunda zan masa.

[Ibrahim Y. Yusuf]

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button