ylliX - Online Advertising Network tsohon sarkin Kano : Yan Nigeria karsu sake su zabe shi a matsayin shugaban kasa Nigeria - AMINCI HAUSA TV
NEWS

tsohon sarkin Kano : Yan Nigeria karsu sake su zabe shi a matsayin shugaban kasa Nigeria

Tsohon sarkin Kano murabus watoh sarki mahammadu Sunusi na biyu ya bayyana cewa kar Yan Nigeria kar suke su zaban wasu Yan takarar shugaban kasa

Muhammad Sunusi na na biyu ya bayyana Hakan ne a wata tattaunawa da yayi a wajen wani taro da aka shirya don nuna farin ciki da haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad s a w

Tsohon sarkin ya bayyana cewa duk wani Dan takara Wanda ya cewa Al umma kasar Nan gyaran kasar Nan abune Mai sauki a wajen sa toh babu shakka kar Yan Nigeria su zabe shi

Ya Kara da cewa gyaran Nigeria abune Mai matukar wahala musamman yadda kasar ke cikin wani irin mahuyacin Hali

Kasar ta Nigeria dai na cikin wani Hali mahuyacin sakamakon yawan karbar bashi da kasar take cigaba da Yi a wannan gomnati

Sarki Muhammad Sunusi ya bayyana cewa yaji wani Dan takara Yan fadin cewa gyaran kasar nana abune da zaiyi a cikin wani karamin lokaci toh kar Yan Nigeria su sake su zabi wanna Dan takara

Sanin kowa ne Nigeria na cikin mahuyacin Hali sakamakon yadda komai yake dada tabarbarewa a kasar Al umma kasar ke cikin mahuyacin halin talauci ga Kuma tsadar rayuwa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button