ylliX - Online Advertising Network Turmin Tsakar Gida: An Yanke Wa Rago Ɗaurin Shekaru Uku A Gidan Yari - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Turmin Tsakar Gida: An Yanke Wa Rago Ɗaurin Shekaru Uku A Gidan Yari

Turmin Tsakar Gida: An Yanke Wa Rago Ɗaurin Shekaru Uku A Gidan Yari

An yanke wa Rago ɗaurin shekaru uku a gidan yari bayan tunkuɗe wata tsohuwa har lahira a Sudan ta Kudu.

An kuma buƙaci mai Ragon da ya ba iyalan wanda aka kashe shanu biyar diyya, kamar yadda wata kotu a birnin Rumbek na Sudan ta Kudu ta yanke hukunci.

A cewar jaridar Sudan Today, ƴan sandan Rumbek a jihar Lakes na Sudan ta Kudu sun kama Ragon bayan ya kashe matar a ƙarshen makon da ya gabata. Rahotanni sun bayyana cewa, Ragon ya kai wa matar hari ta hanyar tunkuɗe ta a ƙirji har ya yi sanadiyyar ajalinta.

A ƙarƙashin dokar al’adar jihar Lakes, duk wani dabbar da ya kashe mutum ana ba shi diyya ga iyalan mamacin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button