LABARAI/NEWS

TUSAR GABAN MACE (QUEEFING KO VAGINAL GAS)

TUSAR GABAN MACE (QUEEFING KO VAGINAL GAS)

Tusar gaban mace: itace fitar da wani iska musamman lokocin jima’i da mijinta, ko idan tayi wani motsin sai taji gabanta yana fitar da wani iska harda kara kamar tusa.

Dalilan da suke kawo wannan tusar gaban sun hada da:

1- Pelvic floor weakness : Sakewar naman cikin farji, idan naman cikin farjin mace ya sake yayi zududu baya iya rike abu yakan kawo wannan matsala.

2- Infection : Shigar kwayar cuta bangaren da ya shafi magaifa ko mafitsara shima yakan haifar da wannan matsala.

3- Feminine hygiene products : chuse-chusen kayan mata, da wassu sabulai marasa asali domin sarkake farji ko matse shi yakan haifar da wannan matsalar.

4- Inserting an object in the vagina : tura wani abun da ba muhallin sa ba suwa cikin farji yakan kawo wannan matsalar.

5- Menopause : Wassu matan suna fuskantar wannan matsalar idan lokocin dauke jinin al’adar su yayi, shekaru arba’in da biyar zuwa sama.

6- Vaginal Fistulas : Wannan idan akan samu tazara ko wata kofar tsakanin hanyoyin da ta hada farji, mafitsara da wajen kashi akan samu wannan matsalar.

Sai Kuma wassu hallayar mu da take taimaka wajen kawo wannan matsalar:

1- Zama a kasa cikin A.C ba wando kuma a kan tiles.
2- Yawo ba takalmi musammanma a AC kuma kan tiles.
3- Kwanciya ki kunna fanka kuma ba wando a jikinki.
4- Rashin yin tsarki da ruwan zafi.
5- Rashin yin tsarki bayan gama jima’i. Wato barin sparm ya kwana a jikinki ba tare da yin tsarki ba.
6- Yawan yin maganin mata ba gaira ba dalili.
7- Rashin iya positioning na kwanciyar aure da miji.
8- Zama da fant guda daya tun daga safe har dare sai kaga mace ta bar fant tun safe har dare yana jikinta tsaban qazanta.

Hanyoyin samun sauki ko waraka:

1- Ayi kokori zuwa asibity domin ganin likita wanda ya kore a bangaren abinda ya shafi mahaifa (Gynaecologist)

2- A kiyaye dukkanin abinda zai kawo wannan matsalar.

3- Adinga yin kagel exercise lokoci bayan lokoci domin naman farji ya samu karfi.

Bayan anje asibity an tabbata matsalolin da muka irga babu daya daga ciki a gwada wannan:

Ki nemi ganyen magarya da gabaruwa, da “ya” yan hulbah. Sai ki hadasu GU daya kina dafawa sai ki Debi gishirin cikin tafin hannunki ki zuba chiki. Sai ki dinga shiga kina seatbirth da shi na tsawon 20 minutes. Sannan ki nemi farin muski sai ki dangwala da auduga me tsafta ki yi matsi da shi.

Allah ya kara mana lafiya.

Lafiya uwar jiki

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button