LABARAI/NEWS

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Taraiya ta ɗage dakatarwar da ta yi wa Twitter

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnatin Taraiya ta ɗage dakatarwar da ta yi wa Twitter

 

Gwamnatin Taraiya ta ɗage dakatarwar da ta yi wa kamfanin kafar sadarwa ta Twitter.

 

Shugaban Hukumar Fasaha da Cigaba ta Ƙasa, NITDA, Kashifu Inuwa ya baiyana haka a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

 

Ya ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya bada umarnin ɗage dakatarwar.

 

Ya kuma ce da ga yau, ƙarfe 12 na dare za a bude kafar ta Twitter.

 

Inuwa ya ƙara da cewa sahaleqr shugaban kasar ta zo ne bayan da Ministan Sadarwa da Ciganan Fasaha, Isa Ali Pantami ya rubuta masa takardar rahoto, inda ya nuna masa dacewar matakin duba da yadda Kamfanin na Twitter ya ke bin ƙa’idojin aiki yanzu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button