LABARAI/NEWS

Uba Ya Yi Wa ‘Yarsa Fyade A Osun, Amma Ya Roki Ta Yafe Masa

Uba Ya Yi Wa ‘Yarsa Fyade A Osun, Amma Ya Roki Ta Yafe Masa

Yansanda a jihar Ogun sun kama wani magidanci dan shekara 53 mai suna Olusegun Oluwole bisa zarginsa da yiwa ‘yarsa mai shekaru 14 fyade

A cikin sanarwar da kakakin Rundunar ‘yansandan jihar Abimbola Oyeyemi ya sama hannu, ta ce, an cafke Olusegun ne bayan yarinyar da wasu da suka yi mata rakiya zuwa ofishin ‘yansanda dake Ibara ta garin Abeokuta ne, sun shigar da korafin na fyade

Sanarwar ta ce, yarinyar ta ce, a daki daya suke kwana da mahaifinsu, inda a wani dare bayan an yi barci “ya janyo ni ya yi min fyade da karfi

Sanarwar ta Cigaba da cewa, Olusegun ya amsa laifinsa bayan da Jami’an ‘yansanda sun bincike shi, inda daga bisani ya nemi afuwar ‘yarsa
Kwamishinan ‘yansanda na jihar Lanre Bankole ya bayar da umarnin a tura maganar zuwa sashen binciken aikata manyan laifuka tare da a tura yarinyar zuwa Asibiti don duba lafiyarta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button