ylliX - Online Advertising Network Video yadda Ƴan Fashin Daji Sun Ƙara Tare Hanyar Katsina Zuwa Jibia - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Video yadda Ƴan Fashin Daji Sun Ƙara Tare Hanyar Katsina Zuwa Jibia

Ƴan Fashin Daji Sun Ƙara Tare Hanyar Katsina Zuwa Jibia yamma Ɓarayin daji sun ƙara saka Shinge akan Babban titin Jibia zuwa Katsina a tsakanin garin Kadobe da Farun Bala.

Daya daga cikin waɗanda abin ya ritsa dasu ya tabbatar mana cewar Muna cikin tafiya sai muka yi karo dasu yayin da suka harbi tayar motar da muke ciki, Wanda hakan yayi silar kwacewar motar daga hannun Direbanmu ta sauka ƙasa,

sannan suka ci gaba da harbin kan Mai uwa da wabi, yayin da suka kashe wani fasinja har Lahira sannan suka raunata wasu Daga karshe kuma Ƴan ta’addar sukayi awon gaba da wasu daga cikin Fasinjojin amma cikin ikon Allah Jami’an tsaro sun kai ɗauki

wasu a cikin motar APC wato Bullet Proof wasu a cikin mota kirar Koker yayin da wasu suke a jirgin sama. kuma sun samu nasarar kutsawa tare da bibiyarsu har cikin dajin

A kwanakin nan dai saka Shinge a hanyar ta Jibia ya zama ruwan dare yayin da lokata da dama kawai sai kaji ance an tarbe hanyar da rana kata, akwai wani ma Ɗan Ta’adar da ake mashi laƙabi da Solar ma’ana dai shi da rana yake fitowa kata ya aikata ɓarnar shi yayi gaba abinshi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button