LABARAI/NEWS

video Yadda Sojojin Nigeria Suka Kama Mai Taimakawa Yan Bindiga

Tukur Mamu na hannun mu in ji DSS
Bayan zargin Malam Tukur Mamu da ake da hannu wurin kai fansar N2b ga yan ta’adda ana zarginsa da alaka mai karfi da wata kungiyar ta’addanci dake yankin Sinai a kasar Misra

Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa Mamu na cikin jerin wadanda hukumomin tsaro a duniya ta sa wa ido saboda alakarsa da kungiyoyin ta’addanci a Sinai Libya da wasu sassan Afirka ta yamma

Hukumar ƴan sandan farin kaya DSS ta ce Tukur Mamu wanda ke sasanci da ƴan ta’adda da su kai garkuwa da fasinjojin jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna ya na hannunta

A yau Laraba ne dai rahotanni su ka nuna cewa jami’an tsaro sun kama Mamu ɗin a filin jirgin sama na Cairo ƙasar Egypt a kan hanyarsa ta zuwa Saudiyya da iyalansa

Sai dai kuma a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na DSS ta fitar a yau Laraba a Abuja hukumar ta tabbatar da cewa ya na hannunta bayan an dawo da shi daga Egypt

Sanarwar ta ce an kama Mamu ne bisa umarnin hukumomin soji da na tsaro da kuma na tsaron sirri domin ya amsa wasu muhimman tambayoyi a kan binciken da ake yi kan yanayin tsaro a wani ɓangare na ƙasar nan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button