Daga Malaman mu

Waƙen Ta’aziyyar Dr. Ahmad Buk (Bomba)

MARSIYYAR DAKTA AHMAD BAMBA

 

Rabbi ke rayar da bawa,

Rabbi Shi ne mai kashewa,

Mumunai ba sa musawa.

 

Ran da duk bawa ya tashi,

Kwanakinsa yake ta ci shi,

Mutuwa na nan matsowa.

 

Annabawa har suhabbai,

Fardan jama’u da dubbai,

Mutuwa ta ɗauki kowa.

 

Yau Kano ta shigo garinmu,

Har ta ɗau shehi gwaninmu,

Yau hawaye mun zubarwa.

 

Yau fa ta ɗau shugabanmu,

Yau fa ta ɗau malaminmu,

Yau fa Dakta yai gushewa.

 

Dattijo mutum na gaske,

Mai kira kullum ga haske,

Mai kiran shiriya ga kowa.

 

Yau mun yi rashin hadisi,

Yau mun yi rashi na nassi,

Yau mun rasa mai biyawa.

 

Yau mun rasa mai tsayawa,

Kan sunna yai kulawa,

Mai kira kan kyautatawa.

 

Shehu Ahmad ɗan Muhammad,

Wanda ba shi kira ga ilhad,

Gaskiya bai tsalekewa.

 

Yau mun rasa Shehu Bamba,

Wanda ba shi kira da gaba,

Wanda bai son mui rabewa.

 

Rabbi Kai rahama ga malam,

Kai shi gun baban su Кasim,

Sa shi Janna gidan sakewa.

 

Rabbi sa shi cikin masoya,

Rabbi sa shi ya san wilaya,

Sa shi zumrar annabawa.

 

Rabbi yafe dukkan kurensa,

Karɓi kyawun aiyukansa,

Rabbi kai ke tausasawa.

 

Rabbi shirya mutan gidansa,

Rabbi kyautata ɗalibansa,

Har zuwa ranar tsayawa.

 

Har mu sadu da shi a Janna,

Inda babu fushi da juna,

In da bai mai ƙuntatawa.

 

Dr. Murtala Uba Mohammed

07/12/2022

10:17pm

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button