LABARAI/NEWS

wacce Irin cuta ce take damun fati bararoji

Wacce Irin Cuta Ce Take Damun Fati Bararoji
Fati Baffa ta ce ta yi mamakin masu surutu game da ita

TUN a safiyar yau Asabar aka fara yaɗa waɗansu hotuna a aoshiyal midiya na jarumar Kannywood Fati Baffa Fagge Bararoji waɗanda su ka nuna Fatin ta yi wata irin ramewa

Ganin hotunan, sai mutane su ka dinga surutu a kan ko dai tsohuwar jarumar ta yi rashin lafiya ne? Idan haka ne kuma, wace irin cuta ce ke damun ta

Binciken mujallar Fim ya nuna cewa asali dai hotunan sun fara bayyana ne a shafin ita jarumar na TikTok da ‘status’, daga nan su ka yaɗu zuwa sauran wasu shafukan na soshiyal midiya

Mujallar Fim ta kira Bararoji ɗin a waya domin tabbatar da halin da ta ke ciki. Mun tambaye ta ko ta na da masaniya kan surutun da ya ɓarke game da ita a soshiyal midiya

Fati ta amsa da cewa Gaskiya na yi mamaki da na ji mutane su na ta surutu a kan wannan hotunan, har ma ake cewa ba ni da lafiya. To ni lafiya ta ƙalau, ban yi rashin lafiya ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button