LABARAI/NEWS

Wallahi Duk Wanda Baiyiwa Mahaifan sa Biyaiya ba Bazai Gama Da Duniya Lafiya ba Khalifa Muhammadu Sanusi II

Wallahi Duk Wanda Baiyiwa Mahaifan sa Biyaiya ba Bazai Gama Da Duniya Lafiya ba Khalifa Muhammadu Sanusi II

Khalipa darikar Tijjaniya na Najeriya, Malam Muhammadu Sunusi II, yaja hankalin alumma akan su dage da ganin sunyiwa mahaifan su biyaiya akan dukkan abun da yake ba sabon Allah.

Sarkin Kano 14 yayi wanda nasiha ne, a yayin da yake gabatar da karatun littafin addinin musulunci mai suna madarijus Salikeen wanda yake gudanar duk mako – mako.

 

 

Khalipan ya baiyyana musifar da dan Adam zai shiga mutukar baya yiwa iyayan sa biyaiya inda yace komai ‘girman mutum da mukamin sa Indai baya biyaiya ga mahaifan sa to tabbas zaiyi mummunan karshe’ .

Basaraken yaci gaba da cewa ‘yana daya daga cikin manyan zunubai shine sabawa iyaye inda kuma yayi kira ga mutane ga duk Wanda yasan yana da matsala da iyayansa to ya gaggauta zuwa ya nemi afuwarsu domin gamawa da duniya lafiya’

A karshe yakare da jan hankalin alumma gami da shaidar zur saboda yadda muta ne suke ta aikatawa a koda yaushe a salo daban – daban.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button