Wani Mummunan Harin Ƴan Bindiga Ya Hallaka Mutane 11 A Ƙauyukan Batsari

Wani Mummunan Harin Ƴan Bindiga Ya Hallaka Mutane 11 A Ƙauyukan Batsari Kimanin Mutane 11 ne suka rasa rayukansu sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai a wasu ƙauyuka a Ƙaramar Hukumar Batsari
Shugaban Ƙaramar Hukumar ya bayyana haka a lokacin da yake mika tallafin kudi ga iyalan waɗanda iftila’in ƴan bindiga ya shafa
Al’ummomin da abin ya shafa sun haɗa da Abadau-Kagara da Garin Zaki da Dadin Kowa da Ƙauyen Ɗanbara’u da Zamfarawa
sun karɓi Naira Dubu Ɗari yayin da waɗanda suka samu raunuka aka basu kudi Naira Dubu Hamsin domin rage wasu matsalolin da suka fama dashi biyo bayan Hare-haren
Daraktan Ilimi da Walwalar Jama’a ya jajantawa waɗanda rikicin ya shafa sai yayi kira ga Jama’a da su kara kaimi wajen gudanar da addu’o’in neman taimakon a kan kalubalen tsaro da jihar ke fuskanta a halin yanzu
Haka zalika Ƙaramar Hukumar ta raba Naira Dubu Goma-Goma ga mutane ɗari hudu Marasa galihu a matsayin Tallafi don bunkasa Kasuwancin su domin su sami abin da zasu rinƙa ci kafin komai ya dai ldaita