LABARAI/NEWS

Wanna Wani Kogi ne dake Arewa Mason Gabashin kasar Senegal yana da nisan Kilometer 35 daga babban birnin kasar wato Dakar

Wanna Wani Kogi ne dake Arewa Mason Gabashin kasar Senegal yana da nisan Kilometer 35 daga babban birnin kasar wato Dakar

Kogin Retba ko kuma ana Kiran sa da Loc Rose Kogi ne da yake da launin Pink ko Ruwan Hoda wani lokacin yakan Canza kamar zai yi Ja (Red) musamman a lokacin Rani

Asalin Kogin Retba yana da tushe ko hanya ko jijiya daga babban Kogin duniya Atlantic Ocean launin sa yakan Canza musamman da daddare daga asalin Pink zuwa Pink light

 

Kogin Yana da tsananin Sinadarin Gishiri High Salty ko Hash Salinity wanda Masana sunce ya kai 40 percent daga 100 wato ya zarce karfin Kogin Mutuwa Dead Sea wanda ke tsakanin Jordan da Israel

 

Mutanen kasar Senegal suna hakon Gishiri daga Kogin wanda duk shekara suke fitar da Ton dubu 24,000 na Gishiri sama da mutum dubu daya ne ke shiga Kogin domin Hakon Gishiri da kuma Suu

 

Sukan shafe Awanni 6 zuwa 7 a kowace rana domin aiyuka a cikin Kogin da gefen sa

Gishirin da ake cirowa daga Kogin ana yawan amfani dashi a zuba a jikin Kifi (Fish) domin Adana shi na lokaci me tsawo bai lalace ba

Duk da cewa karfin Gishirin da Kogin yake dashi Yana cutar da jikin ‘dan Adam, abin mamaki kuma Kifaye suna rayuwa a cikin sa lafiya lau

Ance akwai na’ukan Kifi daban daban a cikin Kogin, wanda ba’a Saba ganin Koguna da irin haka ba

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button