Latest Hausa Novels

WANNAN SARKIN YA BURGENI.

WANNAN SARKIN YA BURGENI.

Wani daga cikin Sarakunan magabata Mai tsananin Adalci da tunani, Shi wannan SARKIN ba musulmi bane.

Lokacin da yazo mutuwa Sai yasa aka kira masa manyan sojojinsa (dogarawansa) sai yace musu, yana son yayi wasu wasiyoyi gudu uku, idan mai yanke kauna (MUTUWA) ta daukeshi.

Wasiyoyin kuwa sune:

  1. Likitocin da sukafi kowa kwareya a fadin kasarsa, su yakeso sudauki akwatin gawarsa sufito da’ita bainar jama’a kafin aje a binneshi.
  2. Dukkan abin daya mallaka na kudi dana zinari ko azurfa, yanason a tattarasu a watsasu a hanyar daza’a bi da gawarsa zuwa makabarta.
  3. Hannayensa kuma yace yana son a barsu a wajen akwatin suna Lilo inda kowa dake wajen zai iya ganinsu (hannayen).

Babba daga cikin sojojinsa sai yayi mamaki game da wayannan Wasiyoyi sai ya tambayeshi dalilin da amfanin yin haka sai shi kuma sai yace:

  1. Inason likitoci su dauki gawa tane domin na nunawa mutane cewa, Idan mutuwa tazo ko da likitocin da sukafi kowa kware wane, baza su iya warkadda mutum ba.
  2. Inason a watsa dukiyata akan hanyane domin mutane susan cewa duk abinda aka samu a
    duniya, a duniya ake barinsa.
  3. Inason abar hannayena suna rito ta wajene domin mutane su gane cewa munzo duniya hannu babu komai haka kuma zamu koma hannunmu babu komai.

INNALILLAHI WA’INNA ILAIHIN RAJI’UN Shin daga Cikin Mu Wanne ne Yake Wannan Tunani?

Hakika Sayyidina Aliyu (RA) Yana Cewa; “Bayanai sun tabbata Cewa, daga lokacin mutuwa zuwa tsayuwa a Gaban Ubangiji akwai Shinge-Shinge na Azaba kuma karami daga cikin Su Itace, MUTUWA”.

Ya Allah Muna Cikin Wata Mai Albarka, Ya Allah duk wanda ya dauki hannun sa Mai daraja Ya Rubuta Ameen Ya Allah Ka Yafe Masa Kura-Kuran sa duka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button