LABARAI/NEWS

WASIƘAR EL RUFAI GA BUHARI Yan Ta’adda Sun Kafa Gwamnati’ A Kaduna

WASIƘAR EL RUFAI GA BUHARI Yan Ta’adda Sun Kafa Gwamnati’ A Kaduna

Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya aika wa Shugaba Muhammadu Buhari wasiƙa mai ɗauke da cewa ‘yan bindiga na ci gaba da kama yankunan karkara su na gwamnatin su tare da kafa sansanin dindindin a dajin Abuja mai kusanci da Abuja babban birnin Tarayya

El-Rufai ya yi wa Buhari
An tabbatar cewa tun a cikin 2012 ‘yan ƙungiyar Ansaru su ka yi kaka-gida a dajin Birnin Gwari, cikin Jihar Kaduna, bayan sun ɓalle daga Boko Haram

Rahotannin sirrin da wannan jarida ta bankaɗo sun nuna mafi yawan munanan hare-haren da aka riƙa yi a baya wanda Boko Haram su ka riƙa ɗaukar alhakin kaiwa, Ansaru ne suka riƙa kai su kafin su ɓalle daga Boko Haram ɗin su Shekau

Masu bincike sun shaida wa wannan jaridar cewa a yanzu ana ƙulla ƙawance tsakanin Boko Haram, JAS, ISWAP, Ansaru da kuma ‘yan bindiga Aƙalla mutum 1,192 ‘yan bindiga da ‘yan ta’adda su ka kashe a Jihar Kaduna

A cikin watanni shidan 2022 kuma idan aka haɗa da kisan rikice-rikicen ƙabilanci, an kashe mutum 645, kamar yadda gwamnati ta bayyana Cikin wasiƙar da El-Rufai ya yi wa Shugaban Ƙasa a watan Yuli, ya yi dalla-dallar yadda ‘yadda su ka kakkama ƙauyuka su ka kafa gwamnati

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button