Nishadi

Wasu Dabi’u Maza Marasa Kyau A Yayi Jima’i

Wasu Dabi’u Maza Marasa Kyau A Yayi Jima’i

Duk da yake ba duk mata bane suke iya fitowa fili su nunawa mazajensu rashin jin dadinsu ba game da wasu halayensu a lokutan sadu da su ba.Sai dai da akwai wasu halayen da maza suke yin su da mata suka tsaka a lukutan saduwa dasu kamar haka: Yawancin maza da zaran sun zo Jima’i da matansu basu damu da su musu wasa ba. Kawai namiji zai juya mace ne kawai ya hau kanta tamkar ya hau kan shingidarsa babu wani wasannin da zai motsa mata sha’awa. Kamin ta gama gyrawa har ya gama ya sauka.Akwai ma mazan da ko kwandonsu basa cirewa saboda tsabar wulakanci da rashin iya sanin kwanciyar aure. Namiji ne zai sauke wandonsa kasa kawai ya hau kan matarsa kamin ta ankara yayi ya gama.Wananna dabi’a yana matukar bakantawa mace rai a lokacinda namiji ya mata hakan.Mace tana son doguwar wasannin motsa sha’awa da zai tayarwa mata jijiyoyin dake jikinta ya sata tsiyaya har sai da kanta ta bukaci miji ya shigeta kamin nan. Amma ba irin cin zakara da rashin sanin hakkin kwanciyar aure da wasu mazan suke yi ba.Bayaga rashin motsa mace, wani abunda mata suka Tsana a lokacin Jima’i da mazansu shine kazanta. Wasu mazan yadda suka dawo daga kasuwa, aiki ko gona haka nan suke afkawa matansu jiki duk wari dauda da zufa.Kamar yadda duk namiji yake son yaga matarsa tayi tsafa kamin Jima’i da ita, haka itama mace take son ganin mijinta.Yana da kyau kamin namiji ya tinkari matarsa da Jima’i ya tabbatar da cewa ya yi wanka. Wankan Jima’i daban yake da sauran wanka. Domin namiji zai maida hankali ne wajen tsaftace golayensa ya wankesu tsaf. Ya wanke matsi matsinsa yadda ya kamata. Ya tabbatar da duburansa ya fita tas. Ya dirje hamatansa zuwa cikin da wajen wuyansa. Ya kuma tabbatar da bakinsa ya goge tsaf.Yi amfani da turare na jiki bana kaya ba a wannan lokacin. Yadda idan matarka ta kwanta a jikinka kamshi kawai zata ji yana tashi ba hamami ba.Muddin namiji ya gaza yin wannan wanka kamin ya kusanci iyali, to gyara kawai ya hakura da saduwa da ita domin cutar da ita kawai zai yi da wari. Shi yasa mata suka tsani maza masu zuwa musu da kazanta a lokacin saduwa dasu. Wani abun takaici da akasarin maza suke yi a lokacin saduwa da matansu shine tashi su barsu bayan sun biya bukatarsu.Mace tana son bayan kun gama jin dadi ku rungumi juna, cike da soyayya da kauna tare da yiwa juna kirari da godiya bayan kun gama. Amma ba kowa ya kama gabansa ba kaman yadda maza masu neman karuwai suke yi bayan sun yi zina.Duk wata mace tana son bayan kammala Jima’i da mijinta tana jikinsa, idan wanka zasu shiga su shiga tare, idan dauraye jiki zasu yi su ci gaba nan ma suyi tare. Amma ba daga gamawa sai wannan ya juyawa wannan baya ba. Mata sun tsani hakan.Da fatan maza zasu fahimci kuskuren da suke tafkawa masu kama da irin wadannan su gyara.

Musamman wajen rashin tsafta da kuma rashin motsa mace da gudu a barta bayan namiji ya gamsu ita bata gamsu ba. Idan hali ya samu zamu kawo darasin da maza ma’aurata zasu gamsar da matansu cikin sauki kamin su Mazan suyi zuwan Kai. Da Kuma dabarun da zaka iya yin zuwan Kai lokaci guda da matarka.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button