Islamic Chemist

Wasu Dalilai Da Zasu Iya Jawo Maka Matunci A Wajen Matarka

Wasu Dalilai Da Zasu Iya Jawo Maka Matunci A Wajen Matarka

Tsangayarmalamtonga

Maza daya suna fuskantar rashin mutuntawa daga wajen matansu. Hakan kuwa bai rasa nasaba da yadda suken yi mu’amala ne da matan nasu.
Ga wasu hanyoyin da zaka iya jawowa kanka mutunci a wajen matarka.

Tsangayarmalam

Idan kana so gayi daraja da mutunci a wajen matarka dole sai ka dauke ta a matsayin matarka ba baiwarka ba.
Wasu daga makon da suka gama cin angwancinsu, daga wannan makon mace ta daina ganin fara’arsu da wasannin da suka saba mata kamin aure.
Muzurai bai sa mace ta mutuntaka sai dai ma ta nisanta kanta da kai kana mijinta. Don haka kuji zaman auren ubangida da baiwa idan kana so kayi mutunci a wajen matarka yi mu’amala da ita a matsayin aure ne ya hadaku ba sayota kayi ba.

Ana samun wasu mazan da suka nemi aurensu da karya da kuma yaudara. Sunyi dace sun aura din ma bazasu daina yiwa matan nasu karya da yaudaran ba.
Daga lokacinda mace ta fahimci yawancin abunda kake fadamata ko kake mata alkawari karyace da yaudara, daga lokacin ka daina daraja a idanuwanta.
Idan kana son ganin kayi mutunci a wajen matarka. Ka ajiye zancen karya ko yaudara daga lokacin da ka aureta ka fito mata a gaskiyance.

Neman Mata ba jawowa magidanci rashin mutunci kadai yake yi ba harma da kaskanci wajen matarsa.
Duk irin yadda ake ganin girmanka a waje muddin har neman matanka ya shaharan da matarka ta sani, bazaka taba yin mutunci a wajenta ba.
Duk wata macen da tasan mijinta na neman mata kuma akwai girmamawa a tsakaninsu, tabbas cikin biyu dole akwai guda. Kodai ita kanta mazinaciyar ce kamar yadda ayar Alkurani ya zo dashi. Ko kuma akwai zaman munafurci a tare da ita. Domin a dabi’ar mace wacce aka auro ma ba dadin abun take ji ba bare wacce zinar da ake yi da ita ya bayyana karara.
Wannan yasa duk namijin da yake harkar neman mata, ya daina tsammanin matarsa ko matansa suna masa kallon mutunci.

Duk namijin da yake son ganin matarsa ta mutuntashi ta girmamashi to shi ma ya mutuntata ya girmamata.
Ita mace cikin sauki take fadawa kaunar mutumin da zai nuna mata mutunci bare kuma ace mijinta ne.
Hakan yasa duk namijin dake fatan ganin ya samu mutunci a gidansa wajen matansa, shima ya kasance yana mutuntasu.

Wani al’amarin dake saurin sa namiji yayi mutunci a wajen matarsa shine yaba mata a duk lokacinda tayi abun yabo. Zugata da kodata a duk lokacinda tayi abun a zuzuta ta. Yi mata addu’ar fatan alheri a duk lokacin data saka farin ciki. Furta mata kalamai na soyayya a duk kullum kana kusa da ita ko nesa da ita.
Muddin zaka kasance namiji mai iya yiwa matansa wadannan abubuwan mutuntaka zai zama dole a wajenta ko da ita ce bata son mutuntaka zuciyarta bazai barta ba.

A duk lokacinda zaka yiwa matarka gyaran wani kuskure data yi ko laifi, muddin zaka nuna mata cikin soyayya da kauna, babu hantara, tsawa ko muzurai, dole be wannan matar taka ta mutuntaka.
Mace bata taba ganin namiji mai duka ko zagi a matsayin namijin mai mutunci. Kada ma ka dauka bakaken maganganun da kake jefawa matanka yana sa su ga mutuncinka.

Tsangayarmalamtonga

Maza da dama suna daukan cewa suna juya matansu da mugayen halaye ne saboda matansu suna tsoronsu. Babu macen da mijinta yake bata tsoro sai dai duk mace tana girmama mijinta da kuma dajashi koda mijin banza ne. Wannan yasa wasu mazan suke ganin tamkar alfarmar suke yiwa mace don haka suna da dama da ‘yancin da zasu iya yiwa matansu kowani irin wulakanci. Wannan kuskure ne babba. Idan kana so a mutunta mahaufiyarka a gidan aurenta, kannenka ko yayyunka ko kuma ‘ya’yanka mata. To a guji yiwa nasu wulakanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button