ylliX - Online Advertising Network Wasu Mahara Sun Kona Gidaje Goma A Wata Unguwa A Kano - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Wasu Mahara Sun Kona Gidaje Goma A Wata Unguwa A Kano

Wasu Mahara Sun Kona Gidaje Goma A Wata Unguwa A Kano

Wasu mahara sun kai farmaki al’ummar Dan Jamfari dake kauyen Barbaji a karamar hukumar Rogo a jihar Kano tare da kona gidaje 10.

Sakataren zartarwa na hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Kano, Alhaji Saleh Jili, ya bayyana a ranar Juma’ar nan cewa hukumar ta jajantawa wadanda abin ya shafa tare da kai musu kayan agaji.

Ya ce gwamnatin jihar ba za ta bar wani abu ba don kamo wadanda suka kai harin domin gurfanar da su a gaban kuliya.

Kayayyakin agaji da aka baiwa wadanda abin ya shafa sun hada da bandir din kwanon rufi guda 10, buhunan siminti 20, fakiti 10 na kusoshi, buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 10, guda 20, masara 20 da gishiri buhu biyar.

Wadanda abin ya shafa sun kuma samu kayan sawa, kayan yanka, bokiti, man kayan lambu da kwali biyar na kayan magi.

Jili ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan jihar sannan ya bukaci mazauna yankin da su zauna lafiya da juna.

Wani mazaunin garin, Malam Magaji Audu, ya ce maharan na dauke da sanduna da katako.

Fiye da mutane 200 daga cikinsu ne suka mamaye kauyen cikin dare suna bi gida-gida suna neman babur dinsu da suka sace Maharani sun yi kokarin daba min wuka a gaban ‘yan uwana kuma na ki fitar da ‘ya’yana wadanda suka ce sun sace babur dinsu kamar yadda suka bukata inji shi.

Audu ya bayyana cewa washegari ne maharan suka dawo inda suka banka wa gidansa da sauran mutane wuta yayin da ‘yan uwansa suka tsere Yan bindigar sun kwashe kayan abinci, kaji, turkey, kayan aikin noma tare da lalata gidaje 10 a kauyen in ji shi.

Hakimin Rogo, Alhaji Muhammad Maharazu, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma yabawa hukumar bayar da agajin gaggawa bisa irin wannan kayyakin na agajin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button