Daga Malaman mu

Wasu Mahimman Wuraren Da Zaki Iya Haduwa Da Mijin Aurenki

Wasu Mahimman Wuraren Da Zaki Iya Haduwa Da Mijin Aurenki

Ga matan da suke zabawa kawunansu mazajen aure, ba cikin sauki bane suke samun mazajen da suka musu ba. Musamman mata ko ‘yan matan da ba sa fita.
Sai dai akwai wasu Mahimman Wuraren da asakarin maza masu neman aure da kansu nan suke gilmawa ko zuwa domin neman matan aure. Wadannan wuraren sun hada da:

1: Makaranta. Makaranta na Boko ko na Addini wurine da maza suke zuwa neman matan da zasu aura.
Hakan yasa duk wata daliba ko kuma mace mai shigowa irin wadannan makarantun domin cudanya da kawaya ta kasance tana da dabi’u masu kyau domin akwai mazan dake bibiyanta bata sani ba.
2: Kasuwa: Duk kankantar kasuwa sai anga mata sunfi yawan ziyartar wajen. Hakan ne yasa maza masu neman aure suke gilmawa ko shiga kasuwanni ba domin sayayya ba sai domin neman dacewa da matar da zasu aura.
Yana da kyau a duk lokacinda mace zata yi shirin shiga kasuwa koda batada bukatar manemi yanada kyau tayi shiga na tumunci kuma ta kasance cikin natsuwa domin akwai mazan da suke nan kasuwan domin neman wacce zasu aura.
3: Asibiti: Anfi kwantar da mata anan. Haka nan mata suke jinyar mara lafiya. Kuma mata sune suka fi yawan zuwa dubiya. Wannan yasa a duk lokacin da zaka shiga asibi zaka dauka kana gidan buki ne saboda yadda mata suke kaiwa da komowa anan.
Da wannan ne kuma yasa maza masu neman matan da zasu aure suke ziyartan asibitoci ko basuda wanda zasu duba domin neman dacewa da macen aure.
Don haka ko jinya kike yi na mara lafiya ko kuma dubiya ki tabbatar kina cikin kamala.
4: Shagunan Sayeyya (Super Market): Nan ma wajene da maza suke kama tasha domin neman matan da zasu aura.
Zaki ga maza nata gilmawa suna ta kaima da komowa kamar masu sayayya yawancinsu dace da matar aure suke yi.
Wannan yasa idan kin shiga irin wadannan shaguna kada ki kama ciye ciye da hauma hauma irin na mata mara natsuwa. Domin akwai masu bibiyanki anan.
5: Bankuna: Nan ma wajena da maza suke zuba idanuwa domin dace da matan da zasu aure.
Kuna iya karo da namiji a ATM ko cikin banki. Hakan yasa ya zama dole ki kasance mace mai iya mu’amala da mutane ta haka ne zakiyi dacen samun mijin aure a irin wadannan wuraren.
6: Keke Napep Ko Taxi. Su bakamar Bus ba suke. Keke Napep Ko Taxi wurare ne da suke da karanci mutane akwai natsuwar da nan take namiji zai iya arba da macen aurensa.
A duk lokacinda mace zatayi amfani da wadannan abun hawa kuma ba ita kadai ba. Ta kasance mai hakuri, da kamun kai cikin shiga na kamala. Saboda zata iya haduwa da mijin aurenta anan.
7: Shafukan Zumunta: Nan ne ma wajen maza suka fi yawan neman matan da zasu aura. Duk da yake ba haduwa kuke da mutum gaba da gaba da farko. Haka kuma wajene da ake samun mayaudara da ‘yan damfara. Hakan bai hana maza masu neman matan da zasu aura amfani da wannan kafar ba.
Don haka da kin fiskanci namiji da gaske yake ba wasa da yazo dashi ba. Ki saurareshi wata kila shine mijin aurenki.

Ana iya samun wasu wuraren kaman wajen buki da daku nan taro ko fati na bukukuwa da maza suke zuwa neman matan da zasu aura. Nan ma macen da take da natsuwa, shiga na mutunci da kamun kai ce kawai zata dauki hankalin mazan da suke nan.
Yana da kyau matan da suke bukatan mazan aure su fahimci cewa babu yadda zasu auru ba tare da sun hadu da mai bukatan aure ba. Ba kuma zasu hadu da masu bukatarba har sai suna ziyartar wuraren da zasu yi cudanya da mutane.
A kullum mace da zata cikin kamala a duk inda take, zata riga matan da suke da rawan ka da shishigewa maza saurin dace da mazan aure.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button