LABARAI/NEWS

Wasu Yan ta’adda Sanye da kakin Sojojin Nijeriya Sun Sace yara Uku a jihar Kwara.

Wasu Yan ta’adda Sanye da kakin Sojojin Nijeriya Sun Sace yara Uku a jihar Kwara.

Wasu ‘yan bindiga da ba’a san ko su waye ba Sanye da rigar Sojoji Sun yi garkuwa da yara Uku a jihar Kwara.

Wasu Mutane Shida da ake zargin Masu garkuwa da Mutane ne Sanye da kakin Sojoji ɗauke da Muggan mMakamai Sun yi garkuwa da Wasu yara Uku a Unguwar Aseyori da ke yankin Alagbado a ƙaramar hukumar Ilorin ta Yamma a jihar Kwara.

An gano cewa Waɗanda ake zargin Ƴan bindiga ne su ka kai hari gidan wani Mutum a ranar Larabar da ta gabata a Unguwar Wanda aka bayyana sunan sa da mai sayar da ƙarafa Lukman Aliyu, “inda Suka riƙa harbin iska.

Lamarin dai kamar yadda aka bayyana ya haifar da hargitsi a tsakanin mutanen yankin yayin da mutane suka tsere domin tsira da rayukansu daga bisani kuma aka gano uku daga cikin ƳanƳan ɗan kasuwar da maharan suka yi awon gaba da su.

Da yake bayyana abin da ya faru da manema labarai a Ilorin wakiliyar mu ta tattaro cewa, mahaifin yaran ya ce kawai ya kashe wutar lantarki ne kawai ya shige cikin duhu ya kwanta sai ya ji wani baƙon hayaniyar maharin da tsakar dare.

Ya yi ikirarin cewa “Sun yi barazanar kashe shi da ’yan uwanss, ni da matata tare da wasu mutane huɗu muka tare kanmu a daƙi ɗaya, amma Ƴan baranda sun shigo gidan suka yi garkuwa da yaran.

lokacin da aka sanar da Ƴan ƙungiyar Ƴan banga a yankin, sun mayar da martani cikin gaggawa inda suka bi sawun masu garkuwa da mutane zuwa cikin garin Shao bayan an sako ɗaya daga cikin yaran ukun da aka sace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button