LABARAI/NEWS

Wata budurwa a fatakwal ta ƙona gidan Saurayinta ƙurmus kan yaudaranta da ya yi.

Wata budurwa a fatakwal ta ƙona gidan Saurayinta ƙurmus kan yaudaranta da ya yi.

A garin Fatakwal, wata budurwa ta ƙona gidan saurayinta bayan ya yaudare ta A fusace wata ‘yar Najeriya ta ƙona gidan saurayinta da ke Borokiri a Fatakwal bayan ta kama shi da wata Suna taɗi

Kamar yadda kafar yada labarai ta yanar gizo ta wallafa, budurwar ta kai wa masoyinta ziyarar ba-zata a gidansa lokacin da ta shiga Sai ta gan shi tare da wata mata

Budurwarsa a fusace ta yaga duk kayan shi da almakashi ta cinna masu wuta kafin ya dawo, rakiyar ɗayan budurwan nashi, Bisani lokacin da saurayin ya dawo gida, sai ya ga gidansa ƙone

Wani faifan bidiyo da ya shaida abin da ya faru a yanar gizo ya bayyana cewa yawancin kayan mutumin da suka haɗa da TV, fanfa, banɗaki, da gado, sun ƙone ƙurmus Daga baya an damke matar kuma aka mika ta ga ‘yan sanda kamar yadda Jaridar tabi diddigin lamarin kuma ta Samu tabbacin hakan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button