Wata mata ta auri saurayi yar’ta a jihar Kano inda hukumar hisba ta halatta auren

Hukumar hisba a nan jihar Kano ta bayyana auren da wata mata ta auri saurayi yar ta a matsayin halattacce lamarin da ke cigaba da janyo cece kuce a fadin jihar ta Kano
Cece kuce na dada zafafa a fadin jihar Kano tun bayan da wata uwa ta kashe auren ta tare da auren saurayin yar ta a jihar Kano
Wannan abu dai ya karade shafukan sada zumunta inda al umma da dama ce tofa albarkacin bakin su kan wannan lamari
Duk da korafi da yar ta shigar gaban hukumar ta hisba amma hakan bai hana soke wanna aure ba inda hukumar ta hisba ta bayyana auren a matsayin halattacce
Da yake zantawa da manema labarai mai magana da yawon hukumar ta hisba labusi Kofar mata ya tabbatar da wanna lamari inda yace auren ya halatta duk da cewa sun sami korafi daga yar ta ta