LABARAI/NEWS

Wata rana mijin wata mata musulma ya mutu.

Wata rana mijin wata mata musulma ya mutu.

Ya mutu ya barmata yara qanana kuma a gidan haya suke rayuwa.

Talauci ya quntata matar, kuma mai gidan haya ya dage akan cewa saidai ta tashi tabar masa gidansa indai bazata iya biyan kudin haya ba.

Haka ta dauki yaranta ta bar garin, don gudun muzgunawar maqiya.

Ta doshi wani garin da yake kusa da garinsu a lokacin da ake tsananin sanyi.

Tana shiga garin sai taga wani tsohon Masallaci wanda an daina Sallah a cikinsa. Sai ta sanya yaranta a cikin Masallacin. Ita kuma ta fito wajen Masallacin ta tsaya tana tunanin yadda zatayi ta samo musu abinci.

Tana tsaye, sai taga wani mutum mai alamar kamala yazo zai wuce.

Mutumin shine limamin garin. Sai matar ta qarasa wajensa tayi masa bayanin halin da take ciki. Ta gaya masa cewa: Ni baquwa ce a garinnan kuma ina tare da marayu. Na shigar dasu cikin Masallacinnan don haka ina buqatar ka taimaka mana da abin da zamuci yau da daddare.

Sai liman yace mata: KAWO MINI DALILIN DA ZAI TABBATAR MINI DA CEWA GASKIYA KIKA FAƊA.

Sai tace: ni mace ce baquwa. Kuma babu wanda ya sanni a garinnan.

Kawai sai limami ya wuce yai tafiyarsa.

Sai ta matsa ta cigaba da tafiya cikin sanyin jiki. Ga sanyin gari.

Tana cikin tafiya sai ta haɗu da wani dattijo. Sai tayi masa bayanin halin da take ciki. Kuma ta gaya masa abinda ya wakana tsakaninta da liman.

Sai dattijon ya shigar da ita gidansa. Ya haɗata da wasu mata sukaje masallacin suka ɗauko y’ay’an wannan matar.

Yasa aka kawo musu abinci na alfarmah. Da tufafi na alfarmah. Suka kwanta a gidansa cikin jin daɗi da girmamawa.

A lokacin da dare ya tsala. Sai limamin nan yayi mafarki. Yaga kanshi a wani waje tamkar a ranar alqiyama. Sai Manzon Allah s.a.w yazo ya sanya masa wata sarqa ta lu’u lu’u akansa sannan liman ya hango wani tabkeken gida na sarauta. Gidan an ginashi da koren Zubardaji. Anyi masa shafe da lu’u lu’u da yaqutu da marjani.

Sai liman ya tambayi Manzon Allah s.a.w yace wancan gidan sarautar na waye?

Sai yace masa: gidan wani mutum ne Musulmi wanda ya kaɗaita Allah s.w.t.

Sai liman yace: ya Rasulullah ai ni mutum ne musulmi. Kuma na kaɗaita Allah.

Sai Manzon Allah yace masa: kawo dalilin da zai tabbatar da cewa ka kaɗaita Allah s.w.t. Ai lokacin da talakar matar nan tazo tayi maka bayani. Kaima cewa kayi ta kawo dalilin da zai tabbatar maka da cewa gaskiya ta faɗa.

Sai liman ya farka daga baccinsa. Cikin nadama da baqin cikin maganar da ya gayama matar nan.

Don haka sai liman ya tashi ya riqa zagaya gari yana kwatantama jama’a matar. Ko wani ya ganta ya taimaka ya nuna masa inda take. Har dai aka nunama liman gidan wani kirista aka gaya masa cewa tana gidan.

Sai liman yaje wajen kiristan yace masa: matar da tazo wajenka da y’ay’anta, a jiya nakeso kabani.

Yace: bazan iya baka ita ba. Saboda Albarkar da na samu. Ta dalilinta.

Liman yace: zan baka Naira dubu 50 domin kabar mini ita.

Kirista yace: bazan iya baka ita ba.

Liman yace: dole ka bani ita.

Sai kiristan yace: abinda kake so ka samu. Nine nafi cancanta dashi. Gidan sarautar da ka gani a cikin mafarkinka an gina gidan ne sabo dani. WALLAHI Tunda nayi mafarkin gidannan na tara iyalina muka musulunta ga bakidayanmu.

Dukkanninmu mun musulunta ne. A hannun wannan matah.

Don haka mafarkin da kayi nima nayishi. A cikin Mafarkin Manzon Allah s.a.w ya tambayeni kamar haka.

SHIN WANNAN MATA DA Y’AY’ANTA SUNA HANNUNKA? Nace: suna hannuna ya Manzon Allah.

Sai Manzon Allah s.a.w yace: to wannan qaton gidan sarautar naka ne kai da iyalanka.

Liman najin haka. Sai ya juya. Cikin matsananci baqin ciki.

ya d’an uwa Alokacin da Allah s.w.t ya baka damar kyautatawa matar da mijinta ya mutu. Ko marayu. To kayi iyakar iyawarka wajen ganin ka kyautata musu.

Ya Allah s.w.t ka kyautata qarshenmu

~USNaj Hassan

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button