LABARAI/NEWS

WATA SABUWA: Bayan sakin waƙar Cass da Warrr Mawaƙi Ado Gwanja ya rera waƙar Luwai

WATA SABUWA: Bayan sakin waƙar Cass da Warrr Mawaƙi Ado Gwanja ya rera waƙar Luwai

Fitaccen mawakin Kannywood Ado Gwanja yana dab da sakin wata waƙa mai suna Luwai

tuni dai mawaƙin ya saki kaɗan daga cikin wakar wacce ake kyautata zaton tafi wadanda ya saki a baya

Tuni dai Al’umma suka fara ƙorafi kan mawaƙin sakamakon sakin waƙoƙi barkatai dake fitar da kalamai waɗanda ba’a saba ji ba

Ko a kwanakin baya ma saida wani lauya ya nemi hukumar Hizba data hana mawakin fitar da irin waƙoƙin da yake masu kama da baɗala wanda kiraye-kirayen da ake ne ma yasa hukumar dake kula da gidajen Radiyo da talabijin ta hana sanya wakar sa mai suna Warr a gidajen Radiyo da talabijin na Nigeria

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button