LABARAI/NEWS

WATA SABUWA: Buhari ya saka hannu kan dokar da ta tanadi: A rika cire haraji a cikin kudin kiran waya domin tarawa a rika biyawa nakasassu kudin asibiti

WATA SABUWA: Buhari ya saka hannu kan dokar da ta tanadi: A rika cire haraji a cikin kudin kiran waya domin tarawa a rika biyawa nakasassu kudin asibiti

Daga Muryoyi

Gwamnatin tarayya ta kafa wata doka da ya bada izini a kara farashin kudin kiran waya a duka kamfanonin sadarwar kasarnan domin ayi amfanin da sabon harajin wurin daukar nauyin kiwon lafiyar ‘yan Najeriya masu rauni da masu fama da Nakasa da sauran masu lalura.

Dokar ta ce idan aka tara kudin za a rika biyawa yara yan kasa da shekara 5, da mata da guragu da mararsa galihu kudaden asibiti.

Muryoyi ta ruwaito wannan haraji yana kunshe ne a cikin sabuwar dokar Hukumar Inshorar lafiya da shugaban kasa Muhammadu Buhari yasa wa hannu a makon da ya gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button