LABARAI/NEWS

YA KAMATA MASU IKO DA NIGERIA SU LURA DA ABINDA YAKE FARUWA A KUDANCIN NIGERIA

YA KAMATA MASU IKO DA NIGERIA SU LURA DA ABINDA YAKE FARUWA A KUDANCIN NIGERIA

An fi sati guda kusan kullun sai kungiyar ‘yan Aware masu fafutukar kafa Kasar Biyapara a kudancin Nigeria sun yi hari akan jami’an tsaro suna nan suna cin karensu babu babbaka babu wani mai challenging dinsu a hukumomin tsaron Nigeria, sunfi karfin kowa

Kuma idan sunyi ta’addanci suna nadar bidiyo su boye fuskarsu su yada, ba wani mai Technology da dabaru wanda ya san movement dinsu yaje yayi encountering dinsu, babu a yanzu

Amma lokacin da DCP Abba Kyari da yaransa suke aiki sun taka musu burki, sun hanasu sakat saboda sun san duk wani dabarunsu da movement din su, shiyasa sukayi ta neutralizing dinsu a lokacin

Yanzu komai ya lalace babu wani competent unit na tsaro da yake iya kalubalantar wadannan tsageru, suna tafiya free abinsu, sun tabbatar da dokar sit at home a duk ranar litinin a yankin da suke da karfi a Kudu

Jiya Maigirma Shugaban ‘yan sanda yana Maiduguri, yayi bayanin cewa a kullun sai ya rasa jami’in tsaro da aka kashe a bakin aiki

Tun bayan harin gidan yarin Kuje, sai Maciya amanar tsaro suka saye jaridu da sauran manyan kafofin watsa labarai suka hana a dinga yada abinda yake faruwa na matsalar tsaro domin su boye wa shugaban Kasa gaskiya

Sojoji da ‘yan sanda ba wanda ya tsira daga harin wadannan mutane, wadanda suke ganin status dina a WhatsApp jiya na saka bidiyo kala uku na attack da mayakan suka yiwa sojoji da ‘yan sanda a jihar Anambra da Imo a gurare mabanbanta, har ofishin ‘yan sanda sun kona kurmus, kullun sai sun kashe jami’an tsaro

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button