Fadakarwa

YA KAMATA MUSULMAI KU HANKALTA DA TASHAR AREWA24

YA KAMATA MUSULMAI KU HANKALTA DA TASHAR AREWA24

Shirin Kwana casa’in na tashar Yehodawa Arewa 24 shiri ne wanda ya ja ra’ayin Musulmin Arewacin Nigeria

Da jimawa Arewa 24 sun tafi hutu, sai gashi jiya sun fitar da sanarwa cewa:
Albishirinku ma’abota kallon Arewa 24 jira ya kare, shirin kwana casa’in zango na bakwai (7) zai fara zuwa muku ranar Lahadi 3 ga watan April da misalin karfe 8:00 na dare

To ku duba ‘yan uwa Musulmi, saboda makirci basu tashi dawo da shirin ba sai da suka dubi daidai da lokacin da za’a fara Azumin watan Ramadan, kuma zasu haska shirin a daidai lokacin da Musulmai ya kamata suyi Sallar Tarawih

Ba komai bane face manufa na shagaltar da Musulmai daga barin yin ibada a lokaci mafi tsada a cikin wata mafi daraja a watannin Musulunci

Muna rokon Allah Ya kare Musulunci da Musulmai daga tanadin Yahodawan duniya

Daga Datti Assalafiy

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button