Yabon Manzon Allah yayi mana komai a rayuwata Hafiz Abdalllah da matarsa

Yabon Manzon Allah yayi mana komai a rayuwata Hafiz Abdalllah da matarsa
Babban sha’iri anan jihar Kano yayin zantawarsa da gidan talabijin na BBC Hausa ya fadi magana akan rayuwarsa da kuma yadda yake jin dadinta cikin wannan harka ta yabon Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallam inda ya fara dayin wakar yabon
Sannan tace shi a yanzu babu wata sana’a daya riƙe kamar yabon Annabi inda yace shine sana’ar kuma shine jarinsa dashi yake komai na yau da kullum
Yace shida matarsa suke wannan wakar kuma har abada bazasu daina ba saboda yanajin dadin wannan lamarin kuma mawakin yana daga cikin manyan masu yabon wanda suke da tarin masoya da kuma kaifin basirar waka
Yace shi fa Acikin wannan rayuwar yabon Annabi yayi masa komai kuma yana kan yi masa bashi da bakin godiya a kullum nasara yake kara gani a harkar yabo
Mawakin mai suna Hafiz Abdullah wanda ba boyayye bane acikin wannan gari kusan kowa yasan shi tunda aminin marigayi fadar bege ne Allah yajikansa