ylliX - Online Advertising Network Yadda ɗan shekara 20 ya bada kwangila a ka kashe mahaifinsa a Yobe Ƴan Sanda - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yadda ɗan shekara 20 ya bada kwangila a ka kashe mahaifinsa a Yobe Ƴan Sanda

Yadda ɗan shekara 20 ya bada kwangila a ka kashe mahaifinsa a Yobe Ƴan Sanda

Rundunar ƴan sandan jihar Yobe a yau Laraba ta tabbatar da cafke wani matashi mai suna Yahaya Sai’du, ɗan shekaru 20 da haihuwa, wanda ake zargi da bada kwangilar kashe mahaifinsa, Saidu Oroh.

Kakakin rundunar, DSP Dungus Abdulkarim, ya shaidawa manema labarai a Damaturu cewa an kama wanda ake zargin ne a Gujba, a ranar Litinin.

Ya ce wanda ake zargin ya dauki hayar wasu mahara uku da suka harbe Oroh har lahira a gidansa da ke kauyen Pompom, a ranar 20 ga watan Agusta.

Bincike ya nuna cewa wanda ake zargin ya biya ƴan bindigar Naira 350,000 don su kashe mahaifinsa, makiyayi, don kawai su yi masa fashin shanunsa.

An gano kwanson harsashi guda uku na bindiga mai baki biyu a wurin kuma ‘yan sanda sun fara bin wadanda ake zargin nan take bayan faruwar lamarin.

Jami’an tsaro, bisa bayanan sirri, sun kama Sa’idu a garin Gujba a ranar 17 ga watan Oktoba, yayin da yake yunkurin sayar da shanu 30 da ya sace daga mahaifin na sa in ji Abdulkarim.

Kakakin ya ce rundunar ‘yan sandan kuma tana bin sauran mutane ukun da suka rage, inda ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za a kama su Ya ce Saidu zai fuskanci tuhuma bayan cikakken bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button