LABARAI/NEWS

Yadda ‘Dan Ta’addan ISWAP ya Samu Gidan Zama, Ya Sayi Filaye 5 da Taimakon Jami’in Hisbah a Kano.

Yadda ‘Dan Ta’addan ISWAP ya Samu Gidan Zama, Ya Sayi Filaye 5 da Taimakon Jami’in Hisbah a Kano.

An gano yadda kwamandan ISWAP da aka kama a nan Kano ya nemi taimakon wani jami’in Hisbah wurin kama haya tare da siyan filaye har biyar a wurare daban-daban a Kano.

A cikin kwanakin nan ne jami’an tsaro suka yi ram da wani ‘dan ta’addan ISWAP a jihar Kano. Ya hada alaka da jami’in hukumar Hisbah a jihar wanda ya taimaka masa ya siya filaye kuma ya kama gidan haya.

‘Dan ta’addan mai sunaye da yawa kamar Malam Abba da Adamu Makeri, ya hadu da jami’in hukumar Hisbah a wani darasin Larabci da yake halarta a Masallacin Almuntada, Masallacin ‘yan salaf dake Dorayi a jihar Kano kamar yadda bayanan jami’an tsaro suka bayyana.

Jaridar nan ta HumAngle mai majiyoyi a harkokin tsaro ta ruwaito cewa, alakar ta bai wa ‘dan ta’addan damar kama haya a yankin Samegu dake karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano na sama da shekaru hudu kafin dubunsa ta cika a farkon watan Yuni.

Wurin yana da kusanci da inda jami’an tsaro na farin kaya suka kama wata mota dankare da makamai.

Bayanin ya bayyana cewa, ‘dan ta’addan ya roki jami’in Hisban da yayi amfani da isar sa wurin sama masa haya bayan bayyana masa da yayi yana kwana a wata ma’ajiyar kayayyaki ne.

Daga bisani ya sanar da jami’in cewa zai kwaso iyalansa daga jamhuriyar Nijar kuma yana neman taimakonsa wurin samun wani gidan haya.

Jami’in Hisban yace “A lokacin da muka hadu, yace min shi dan kasuwar ne kuma yana kai takalma da sutturu Nijar.

Bani da wani karin bayani akan miyagun ayyukan shi,”

Taimakon jami’in ne ya bai wa ‘dan ta’addan damar samun haya ba tare da ya bi tsarikan da jihar ta gindaya ba wurin karba ko bayar da hayar gidaje.

Wani ‘dan kungiyar wanda yace ‘dan uwansa ne daga Nijar daga bisani ya dawo zama tare da shi.

Ya yi amfani da alakarsa da jami’in Hisbah wurin siyan filaye biyar a wasu wurare a jihar.

Masu unguwanni a Kano sun yi korafin cewa masu gidajen haya da ejen suna tsallake su wurin bada haya ko siyar da gidaje ga jama’a da ba a sani ba, lamarin da ke kawo hatsari.

Da yan jarida suka tuntubi wata mazauniyar karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano mai suna Hajiya Zainab Abubakar kan al’amarin.

Ma’aikaciyar bankin mai ‘ya’ya 4 ta bayyana tsoro da tashin hankalin da suka shiga bayan samun labarin Malam Abba da kamensa.

Tace “A gaskiya mun fada tashin hankali, ganin cewa abinda muke ji a nesa gashi ya zo kusa da mu.

Akwai bukatar mu kiyaye kan wadanda za mu bai wa haya ko siyarwa da gidaje domin gujewa fadawa hatsari.

Gwamnati ta riga ta gindaya sharudda da dokokin bayar da haya ko siyar da gidaje.

Kamata yayi duk matsuwar da mutum ya zo maka da ita, ballantana bako, ka tabbatar an bi wadannan ka’idoji.
.
Allah ya kare mu, ya zaunar da kasar mu lafiya inji ta.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button