ylliX - Online Advertising Network Yadda Duban-Dubatar Al'ummar Musulmi Sun Gudanar Da Zagayen Maulidin Manzon Allah (S A W) A Garin Zuru Da Ke Jihar Kebbi, - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yadda Duban-Dubatar Al’ummar Musulmi Sun Gudanar Da Zagayen Maulidin Manzon Allah (S A W) A Garin Zuru Da Ke Jihar Kebbi,

Yadda Duban-Dubatar Al’ummar Musulmi Sun Gudanar Da Zagayen Maulidin Manzon Allah (S A W) A Garin Zuru Da Ke Jihar Kebbi,

Al’ummar musulmi mabiya Darikar Tijjaniyya sun gudanar da taron zagayen maulidin Manzon Allah (S A W) domin tunawa da ranar da aka haifi Manzon Allah (S A W)

Yadda aka gudanar da zagayen maulidin Manzon Allah (S A W) a birnin Zuru da ke jihar Kebbi a arewacin Najeriya, inda duban dubatar al’ummar musulmai ne suka halarci taron zagayen,

Dan dazon duban dubatar jama’a kenan mabiya Darikar Tijjaniyya wanda suka halarci babban taron maulidin Manzon Allah (S A W) wanda yake gudana yanzu haka acikin garin Zuru,

Ranar zuwan Manzon Allah (S A W) duniya itace babbar ranar zuwan mafifincin halitta mafi soyuwa a wurin Allah akan dukkanin talikai akan haka wannan rana ce mai matsayi da daraja a wurin dukkanin masoya Manzon Allah (S A W),

Rahotanni sun tabbatar muna da cewa sama da daliban islamiyoyi dubu Goma ne suka fito manyan su da yaran su mazan su da matan su domin taya murna da samuwar Annabi Muhammad (S A W)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button