Yadda Hadiza Gabon ke koyawa yar’ta Maryam ayyukan Alkhairi da takeyiwa talakawa

Yadda Hadiza Gabon ke koyawa yar’ta Maryam ayyukan alkhairi da takeyi na kyauyuka
Jarumar kannywood Hadiza Gabon tana cikin jarumai masu gidauniya ta taimakawa mutane wacce ake taimakawa marassa karfi da musamman wa’yanda suke kauyika da birnin duk dai masu bukatar taimako jarumar tana kokari wajen taimakawa mutane wanda hakan yake kara mata farin jini da mutunci a idon mutane
Sai gashi alokacin da take wannan aikin alkhairi aka ganta tare da yarta wanda hakan ke nufin tana nunawa wannan yarinyar yadda ake aikin alkhairi koda ta girman daman ta samu kulawa ta yadda zata taimakawa marassa karfi da talakawa wannan tarbiyya ce me kyau sosai
Sai dai wasu na sukan abin ta yadda suke cewa wannan jarumar nayin wannan abinne saboda idon duniya kawai bawai dan Allah amma kuma anyi kira ga mutane dasu kula wajen daina mummunan fahimta ga bayin Allah masu alkata abun alkhairi
Dimin yin hakan kamar zai dakile wasu abubuwan ne ya kuma saka mutane su daina tausayi da taimakawa mutane domin kamar karya gwaiwar mutane ne hakan
Jarumar tace ita idan tana aikata wani abu bata kallon surutan mutane kawai tanayi ne don Allah bawai da mutane su yaba mataba hakika wannan halin jaruamar abin koyi ne ga ragowar jarumai da kuma mutane masu hali