ylliX - Online Advertising Network Yadda masu garkuwa da Mutane suka yi awon gaba da mutane 8 a garin zariya. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yadda masu garkuwa da Mutane suka yi awon gaba da mutane 8 a garin zariya.

Yadda masu garkuwa da Mutane suka yi awon gaba da mutane 8 a garin zariya.

A Daren jiya Lahadine ayarin masu garkuwa da mutane suka shiga wani Anguwa da ake kira da Anguwar Sarkin rafi dake bayan asibitin ƙofar gayan birnin Zariya inda suka tattara Mutane ɗai-ɗai har takwas rigis.

Lamarin ya faru a yau Litinin domin jiyo haƙiƙanin abinda ya faru, inda wakilanmu suka samu damar zantawa da mutum ɗaya mai suna Aliyu Umar wanda ya kuɓuta bayan sun kamasa a daren na jiya Lahadi.

A cigaba da zantawa da shi Aliyu Umar wanda aka fi sani da (Ɗan lami), ya tabbatar mana cewa masu garkuwa da Mutanen sun taresa ne da wurin misalin ƙarfe 10 da kwata na dare, a cikin su wasu sanye da kakin sojoji suka taresa yana kan hanyarsa ɗoɗar ta komawa gida.

Bugu da ƙari bayan sun kamasa sai suka ɗaure hunnunansa, sai dai a lokacin da suka kamasa ɗin ya tarar da akwai wasu mutane uku da suka kama kafin shi, akwai wasu mata da miji da kuma wani wanda bai san saba.

to ana cikin haka sai aka kira wayansa sai suka katse kiran suka kashe wayar bayan sun kwashe Ƴan kuɗaɗen dake jikinsa, sai suka fara tabbayarsa ina ne gidansa yake ? kuma menene sana’arsa ? to da ya gaya musu cewa shi talakane kafintane sana’arsa sai suka ce to za su gidansa.

Ana cikin haka sai wani daga cikin su masu garkuwa da mutanen yayi mai magana amma da yare irin ta filatanci bisani sai yaga ya ƙyalesa da tambaya, can kuma sai yaga an kawo wasu mutane uku tare da wani Alaramma, sai suka zama su takwas camma sai suka ƙara kawo wani daga nan ne suka zama su tara, sai suka ɗaure hannayen kowa a cikinsu suka tasa su gaba shi dai yanata karanta abin da Allah ya horemasa daga bakinsa.

Ɗanlami ya cigaba da bayani kamar haka, adadin masu garkuwa da mutanen ɗin su takwas ne, uku ɗauke da Adduna Biyar ɗauke da bindigu kuma duk cikarsu matasane basu wuce shekaru 20 20 ba.

Har wala yau a cigaba da zantawarsa da wakilan na mu da shi ɗin, yaka da baki inda yake cewa domin wallahi In da ba din bindigar hannun suba duk wanda ya daka babu mai iya tashi cikin su, ana haka bayan sun ta sa su a gaba sai ya fara murɗe hannuwansa har ya iya kwance igiyar, amma sai bai nuna musu cewa ya kwance ba ya rike igiyar to bayan sunzo dab da wata gonar dawa sun raɓeta kawai sai ya yi cikinta a guje wasu daga cikinsu suka bi shi yana gudu yana faɗuwa da haka dai Allah ya tsirartar da shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button