ylliX - Online Advertising Network Yadda Mijina Ya Ɗana Mini Tarko Da Abokinsa - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yadda Mijina Ya Ɗana Mini Tarko Da Abokinsa

Yadda Mijina Ya Ɗana Mini Tarko Da Abokinsa

Mijina ya jima yana zargina ina neman maza, amma duk lokacin da ya zo mini da irin wannan tuhumar sai mun hau sama mun sauko Na numa masa sam ba haka bane

A gaskiya ina neman maza ba karya mijina yake mini ba Hakan kuma ya samo asali ne saboda yadda nake da son abun duniya
Mijina ma’aikaci gwamnatin Tarayya ne ya kuma kai matsayin mataimakin daracta Hakan yasa babu abunda mijina bai mini kama daga ciyarwa har da kula da hakkin yaran da muka haifa

Muna da yara biyu mace ita ce ta farko sai namiji shine na biyu Sai dai duk da ‘yar tawa ta soma tasawa naki yarda na saduda Bani da wata kawa ta kusa dani bare ma tasan abunda nake ciki har ma ta sani ta tona mini asiri ko kuma ace itace take zugani nake bin maza da Aurena

Bana bin duk namijin dana fahimci bai da abun hannunsa Zuwa nake kantunan cin abinci irinsu KFC Chicken na samu waje na zauna. Duk da na haihu muddin ba sani na mutum yayi ba babu yadda za a yi mutum yace na taba aure bare ma ace na haihu. Wannan yasa idan dai zan fita to tabbas bazan dawo gida ba sai na kwanta da namijin da ba nawa ba Wannan yasa na zama duk wani abunda yafi karfina nan take nima nafi karfinsa

Na soma biyawa ‘yan uwana dana kusa dani bukatunsu. Sai dai gida dana sayawa uwata da aikin Hajji dana biyawa kaina da mahaifiyata shine abunda ya tayarwa mijina hankali ya nemi sanin inda na samu kudin yin wannan hidimar. Akan hakan ne sai da muka rabu da mijina na koma gidan mu. Watanni biyu da sakina aka shiga tsakani ya dawo dani

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button