LABARAI/NEWS

Yadda sojojin Nijeriya suka yi galaba akan Mayaƙan boko haram a Neja

Yadda sojojin Nijeriya suka yi galaba akan Mayaƙan boko haram a Neja

Bayanai dai na kara fitowa game da mummunar arangamar da jami’an tsaron sojin Najeriya suka yi da mayakan kungiyar Boko Haram a yankin karamar hukumar Borgu ta jihar Neja,

Rahotanni daga Najeriya na cewa rundunar sojin kasar sun halaka akalla mayakan Boko Haram takwas a jihar Neja da ke tsakiyar arewacin kasar,

Ko da yake har ya zuwa lokacin hada wannan rahoto babu wani karin haske daga jami’an tsaro na Najeriya akan wannan al’amari da ya faru a ranar Lahadin da ta gabata,

Amma rahotanni sun tabbatar da cewa baya ga mayakan da aka kashe sojojin Najeriya sun yi nasarar cafke wasu manyan kwamandojin kungiyar biyu,

Kwamishin kula da harkokin tsaron cikin gida na jihar Neja Mr, Emmanuel Umar ya tabbatar da aukuwar lamarin sannan ya bukaci jama’a su baiwa jami’an tsaro hadin kai,

Shugaban karamar hukumar ta Borgu Hon Ahmed Baba Suleiman Yumu ya ce mayakan na Boko Haram sun kai hari ne da nufin kubutar da yan uwansu da ke kulle a gidan yarin barikin sojin sama da ke Wawa ta yankin kai inji amma sai sojojin Najeriya suka samu nasarar kawar dasu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button