LABARAI/NEWS

Yadda Wani Malami Yake Wahalar Da Ya’yan Mutane Yake Turasu Bara.

Labarin da ya motsamin Zuciya.Yaro ne karami wanda a fuska ban yi zaton ya haura
shekara 8 ba,amma mahaifin sa ya turo shi Kano almaji cikin o da daga garin Gamawa a jihar Bauchi

Ba Zuwan sa almajirancin ne yafi damu na ba,domin
wannan Ai an saba,amma na farko kankantar yaron
nan abar dubawa ce, gashi ilahirin jikin sa yayi kaca
kaca da tabbai na dukan bulala,gaskiya wanda yayi
masa wannan dukan bashi da tausayi kuma bai
cancanci ya amsa sunan Malam ba.
A jawabin da yake bani.yaron ya ce Malamin sa ne
yake dukan sa saboda idan yaje bara baya kawo
masa komai,wai ashe idan an fita bara sadakar farko ta Malam ce.

Yaron yaci gaba da cewar mahaifiyarsa ta rasu kuma
mahaifinsa ne ya kawo shi almajiranci.kuma yace bai
San unguwar da makarantar tasu take ba, kwana biyu
kenan ya fito bara yayi batan kai ya kasa gane makarantar tasu.

Dan Uwan mai unguwar kofar mata mai suna
Hussaini shine ya karbi yaron daga hannun wadanda

suka tsinto shi. Yanzu haka dai mun hada su da Sani

Bundin wani matashi jajirtacce dake tsayawa marasa
gata,na kuma hada su da hukumar yaki da Bara ta
jihar Kano karkashin Sheikh Muhammad Al Bakri

mikha’el domin a dauki mataki na Gaba.
Babban abin takaici ne ace har yanzu a Kano Ana
karbar irin wadannan mini minin yaran da sunan an
kawo su bara gaskiya bai dace ba.
Yanzu wannan yaron dai ba a nuna masa jin kai
ba,bai samu shakuwa da iyaye Ko yan Uwa ba,idan ya
girma a titi wa kuke tunanin zaitausayawa?
Barin irin wadannan yara da muke gani suna gararamba a titi babbar masifa ce,WAcce idan ta
tunkaro bazata takaita akan wanda ya jawo ta kadai
ba,ya kamata mu ribanya kokari wajen yaki dawannan annoba.

Zamanin da da na yanzu ba daya bane.
Ina goyon bayan karatun alkur’ani kuma ina goyon
bayan hana bautar da kananan yara
Allah ya kawo mana karshen matsalolin dake damun Mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button