LABARAI/NEWS

Yadda Wasu Marasa Fahimta Ke Kokarin Bata Wa Minista Sheik Pantami Suna

Yadda Wasu Marasa Fahimta Ke Kokarin Bata Wa Minista Sheik Pantami Suna

 

Na ga Wasu marasa fahimta wadanda kullum ba a jin alkairi daga bakin su sai sharri suna yada wannan hoton wai Malam yasa kuros

 

To idan dai mutum ba màhàùkaçi bane muddin zai tsaya ya duba da kyau zai fahimci komai

 

 

Muddin dama mutum ba sharri ne a zuciyar sa ba kowa ya san Malamin Addinin Musulunci kamar Sheikh Isah Ali Pantami ba zai yi wani abu da zai zamo koyi ga wanda ba musulmin kwarai ba bare wanda ba ma musulmi ba.

Duk wanda ya kalli wadannan hotunan ya san biro ne da kuma kwalliyar jikin aljihu.

Malam Pantami kullum cikin ayyuka na yabawa da jinjinawa yake, amma ba ku yadawa saboda su wadannan alkairi ne amma ku kokarin ku shine ku bata masa suna.

Idan kuka hakura ma kwana nawa ne ya rage ya sauka daga Ministan? Sai ku kawo wanda kuke ganin ya fi shi wanda ba malamin Addinin mu ba tunda Malaman addinin musuluci ba su cancanci Minista ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button