Islamic Chemist

Yadda Za A Samu Fatar Fuska Mai Sulbi

Yadda Za A Samu Fatar Fuska Mai Sulbi:

AMINA ABDULLAHI, YOLA

Assalamu alaikum, barkanmu da sake haduwa da ku a cikin wannan fili namu na kwalliya.

Kamar yadda ake cewa “riga-kafi ya fi magani” don haka ne a yau na kawo muku hanyoyi biyar da za a bi domin kare fuska daga fesowar kuraje da wasu cututtuka.

Yana da kyau mace ta fi kulawa da fuskarta fiye da komai a jikinta. Domin, kafin a hango komai a jikinta, fuskar za a fara hangowa.

Ana iya yi wa fuska tausa.

Kamar yadda kowace gaba a jiki ke son tausa, haka fuska ma tana son ana yawan yi mata tausa kamar sau daya a rana.

Yin tausa ga fuska na taimakawa wajen kara karfin fuska da kuma kare ta daga yankwanewa da wuri a lokacin tsufa.

A kasance ana yawaita wanke hannu.

Domin hannu na dauke da wasu cututtuka da idanu ba su gani. Ya kamata ana wanke hannu sosai a kullum kafin a wanke fuska da shi ko kuma a shafa mata man fuska.

Idan hannu mai dauda ya hadu da fuska, hakan zai haifar da wasu kwayoyin cuta a fuskar.

Kafin a shafa wani mai a fuska, yana da kyau a bude ramukan gumi a fata.

Kuma hakan zai yiwu idan ana wanke fuskar da ruwan dumi, ko a saka tawul a ruwan zafi sai a goge fuskar da ita sannan a shafa man.

Yin haka na taimaka wa man fuska aiki sosai ba tare da bata lokaci ba.

Yana da kyau kafin a wanke fuska a goge ta da magogin fuska.

Yin haka na fitar da matacciyar fata da ta daskare a fuska. Bayan haka sai a wanke ta.

Magogin fuska daban yake da magogin hakori, don haka, za a iya samun magogin fuska a manyan kantunan da suke sayar da kayan kwalliya.

Sannan kada a sake a yi wasa da cin abinci mai dauke da sinadarin ‘calcium’ kuma a rika shan maganin da zai kara wa kashinmu karfi.

Yawan shan ‘calcium’ zai hana fuska fita daga kamanninta na da koda an tsufa.

Shi ka karanta wannan

MAGANIN ZAFIN KISHI GA MATA

Amfani da lemun tsami wajen gyaran fata

Dalilin da ya sanya matan Hausawa ke tsufa da zarar sunyi aure

Islam & Science: THE MOSQUITO

Yadda Mata Za Su Gane Miji Nagari

Shawarwari 52 Zuwa Ga Matan Aure, Zawarawa Da ‘Yan Mata –

https://amincihausatv.com/376-2/

ILLAR JINKIRTA FITSARI ALHALIN KANAJIN FITSARIN

Amfani 9 na bawon ayaba ga lafiyar Dan Adam

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button