Daga Malaman mu

Yadda Zaka Koyi Yiwa Mutanen Da Suka Bata Maka Rai Afuwa

Yadda Zaka Koyi Yiwa Mutanen Da Suka Bata Maka Rai Afuwa

Nasiha

“Waɗanda suke ciyarwa a cikin sauƙi da tsanani kuma suke mãsu haɗiyẽwar fushi, kuma mãsu yãfe wa mutãne laifi. Kuma Allah Yana son mãsu kyautatãwa.” Alkurani 3-134
Da wannan ayar ne zamu ga cewa Allah (SWT) Yace yana son masu hadiyar fushin su kuma masu yafewa wadanda suka bata musu rai.
Ghafara ko Al-‘Afuw da aka ambata kusan sau 5 a cikin Alkurani, kalmomi ne na Larabci da suke nufin yafiya ko hakuri, kauda kai ko kuma a Hausar zamani Shariya.
Yafiya shine mutumin da aka batawa rai, bisa Ganganci ko rashin sani ya cire abunda daga cikin zuciyarsa ya daina ganin wanda ya masa wannan abun da laifin bata masa rai da yayi. Ya hakura sannan ya yafe masa.
Sai dai Yafiya ba abu bane mai sauki ba, musamman ga mutumin da aka bata masa rai ta nau’in cin amana. Yanada jimawa kamin ya yafe, kuma sai mutum ya daure zai iya yafewa. Sai dai kuma ba duk abunda zaka yafe bane zaka iya manta shi ba. Rashin mantuwar abun a zuciyarka ba laifi bane. Amma da zaka iya mantawa da al’amarin shi zai fi domin kada shedan ya rika tunatar da kai ya fama maka ciwon baya.

Tunatarwa

Duk Dan Adam mai laifi ne, mai batawa wanin Allah ne yana sane ko kuma bisa kuskure. Haka nan yana batawa Allah kusan a duk wata dakika, awa, yini, ko a mako. Haka nan yana neman afuwar Allah bisa laifukan nasa da fatan kuma Allah Ya karbi tubansa Ya yafe masa. Da wannan zai duba shima ya yiwa mutanen da suka bata masa afuwa ya manta idan zai iya.
Tunda abune mai matukar wuya musamman ga wanda aka masa laifi mai girma, duk da haka ga wasu matakan da zaka bi domin ganin ka koyi yiwa mutanen da suka bata maka afuwa.

Afuwa

1: Ka Sake Duba Laifin Da Aka Maka: Ka sake duba laifin da mai neman afuwar yayi maka. Laifi ne na Ganganci, cin Amana ko kuma na kuskure ne.
Ka kuma auna laifin ka gani, ka taba yiwa wani ko wasu irinsa suka yafe maka. Ko kuwa har yanzu suna kullace da kai.
Wadannan abubuwan dubawan sune zasu baka damar sanin irin afuwar da zaka masa.
2: Dubi Tasirin Daka Samu: Akwai wani tasiri ko alfanun da fushin da kake yi da wannan ya Amfanar dakai ko kuma kawai kunar zuci kadai kayi ta fama da shi.
Ka auna idan kaine ka nemi gafaran laifin da kayi wa wani yaki yafe maka yaya zakaji.
3: Ka Baiwa Masu Shiga Tsakani Dama: Ana iya samun wanda yayi laifin nan ya turo wasu su baka hakuri. Akasarin irin wadannan mutanen kuwa wadanda kake jin kunya sune. Ba dole bane kai tsaye ka hakura ba tare da ka furta bacin ranka garesu ba.
Haka nan ba dole bane sai shi mai laifin sai yazo gabanka ya durkusa ya nemi afuwar ka ba. Kana iya bayyanawa masu shiga tsakanin matsalarka da shj, afuwar da ka masa, idan akwai wani sharadi bayan afuwar kuma su zama sheda.
Yana iya yuwa ka yafe masa, amma ka daina hulda da shj. Idan matarka ce kana iya yafe mata, amma sai ta gyara kaza ko tayi kaza saboda masu shiga tsakani su sheda.
4: Wanda Yaki Bada Hakuri: Akwai mutanen da koda sun bata maka yanada wuya su iya baka hakuri akan abunda suka yi maka. Wasu saboda girman kai, wasu kuwa suna ganin abunda sukayi bai kai na bacin rai ba.
Idan har ka hadu da irin wadannan mutanen. Abu na farko da zaka soma la’akari da shi ne wani irin mutanen su. Masu girman kai ko dagawa ne, ko dai marasa hankali ne ko shaye shaye. Ta haka ne zaka dubi matsayar da zaka ajiyesu domin ka samu sanyi a ranka yadda zaka yafe musu koda kuwa basu nemi afuwarka ba.
5: Wanda Ya Bata Maka Manta: Dayawa mutanen da suka bata maka rai suna saurin mantuwa da abunda suka maka na bacin rai. Sai dai kai kuma sun barka d jin zafin abunda suka maka da kullum abun zai rika damunka hakan kuma yana taba lafiyarka da rayuwar ka.
Kayi afuwa abun ya wuce ka cire shi a ranka shine maganin cutar da kanka ga wanda yayi sanadiyar hakan ma ya shiga harkokinsa.

Afuwa

6: Zai Iya Lalata Zumunci: Rashin afuwa yana iya lalata zumunci ko alaka.
Idan ma wanda yayi maka baka da zumunci ko alaka da shi, wadanda ya shigo dasu tsakiyar magana suna da shi. Rashin amincewa da bukatarsu zai iya lalata maka alakarka ko zumuncinka dasu.
Haka idan danda ka haifa ne ,Kaninka, ko wanka ko matarka, nan ma kana iya samun matsalar dasu muddin kaki afuwa ga wanda suka nemawa.
7: Yana Baiwa Shedan Dama: Kamar yadda muka kawo jawabi a baya. Rashin yiwa wanda ya maka laifi ahufa damane da kake baiwa shedan na yadda a kullum zai nemi bata maka rai da wannan abun, ya kuma saka gaba da wanda kaki yiwa afuwan.
Amma kana yafe masa koda baza kayi mu’amala da shi bane bazaka yi gaba da shi ba. Haka kuma baza ganshi ciwon bacin ran ya motsa ba
8: Kin Bin Umurnin Allah: Duk da yake rama cuta ga macuci ibada ne, ma’ana ba laifi bane idan har zaka iya ramawa dai-dai da yadda aka maka. Sai dai kwadaitarwan da Allah Yayiwa masu yafiya da yin hakuri yafi na ramawa lada.
Haka nan mafi yawan masu rike da laifin da aka musu a zuciya sukan janye wasu abubuwa na alheri da suka saba yiwa wadan suka bata musu. Ga gaba, ka kuma rashin lada da aka saba samu.
Domin Allah Yana cewa “Kuma kada ma’abũta falala daga gare ku da mawadãta su rantse ga rashin su bãyar da alhẽri ga ma’abũta zumunta da miskĩnai da muhãjirai, a cikin hanyar Allah. Kuma su yãfe, kuma su kau da kai. shin, bã ku son Allah Ya gãfarta muku, alhãli Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai? “
24:22
Don haka duk wanda ya auna wannan umurnin da falalar yin afuwa da ci gaba da yiwa wanda ya Bata Maka alherin daka saba yi ba zaka daina yin aiyukan alheri ba ga wadanda suka bata maka ba.
9: Ka Maida Hankalinka Akan Abunda Kake Yi: Ka dawo da hankalinka akan abunda kake yi zai sa ka manta da laifin da aka maka idan ka yafe. Haka nan rashin yin afuwan na iya shafar abunda ka saka a gaba domin yadda al’amarin ya tsaya maka a rai dole kuma ya shafi al’amuranka na yau da kullum. Hakan kuwa cutuwa ne a gareka ba alfanu ba.
Amma kana yafewa masa zaka manta da abunda saboda harkokin gabanka.
10: Samar Da Cikenken Lafiya:. Baya ga kusantar ka ga Allah. Yiwa Mutane afuwa yana karawa mai yinsa lafiya.
Idan ka kula da yadda zaka hana kanka bacci, saboda wani ya bata maka, hakan ya iya jawo maka hawan jini da taso da wasu cutukan da rashin baccin zai iya jawowa.
Baya ga hawan ciji rashin yin afuwa na sa ciwon zuciya da kuma nakasa garkuwan jikin mutum.
Don haka da zaran mutum ya zabi ya yiwa masu bata masa afuwa a kullum za a rika ganinsa cikin koshin lafiya da walwala.

TsangayarMalam

Tabbas yiwa mutanen da suka bata maka ko sun nemi afuwa ko basu nema ba bai da sauki a musu afuwa. Sai dai kuma dauriyan yin afuwan yafi rashin yin alfanu.
Akwai wasu mutanen da gangan kawai suke bata maka rai domin su dagula maka lissafi ta hanyar bata maka rai. Muddin suka fahimci baka damuwa sune ransu zai soma baci maimakon naka.
Haka nan duk mutumin da ya maka abubuwa bacin rai bisa kuskure ko da ganganci kace ka yafe masa. Wannan mutumin zaka kara kima a wajensa koda kuwa makiyinka ne shi.
Da fatan zamu daure mu rika yiwa masu bata mana afuwa. Ita duniyan ba wani lokaci mai tsawo ake rayuwa cikinta ba don haka rike bacin rai da kin yiwa juna afuwa ba abun alheri bane a duniyan mu da lahiran.
Allah Ya bamu zuciyan yafewa junan mu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button