ylliX - Online Advertising Network YADDA ZAMAN KOTUN KASUWANCIN ONLINE YA KASANCE - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

YADDA ZAMAN KOTUN KASUWANCIN ONLINE YA KASANCE

YADDA ZAMAN KOTUN KASUWANCIN ONLINE YA KASANCE

Jiya Talata ce babbar Kotun Shari’ar Musulunci dake kofar kudu a Kano tacigaba da sauraren karar nan ta kasuwancin Internet tsakani Hajiya Lima da kawayenta na kasuwanci wannan zaman shi ne zama na hudu 4 da aka yi

A zaman kotun Lauyoyin Lima sun Shaidawa kotu cewa ita Hajiya Lima bayan ta karbi kudaden mutane ta yi order kaya daga kasar China amma sai aka kawo mata kaya wadan da basu ta yi order ba sai ta yi korafi a ofishin jakadancin China na kasar nan daga nan sai aka mayar da kayan don a canjo kayan shi ne har yanzu ba a kawo kayan ba aka samu tsaiko

Alkali ya waiwayi abokan kasuwanci Hajiya Lima akan ko me zasu ce sai suka ce suna da hujjar da zasu nuna na zunzurutun kudin da suka turawa Hajiya Lima

Akali ya ce ya dogara da Nafsin Littafin tufa a zama na gaba za a nemi ita Lima ta biya kudin da ake bin ta in ta gamsu ana bin ta kudin in kuma bata gamsu ba sai ayi maganar kawo Hujjah a yayin zaman kotun Matan da suke bin Lima kudi daga Sauran jihohi sun Halarci zaman

Akwai Rashida daga jihar Bauchi mai bin Million 19 akwai Bintu Adam daga Yobe mai Million 6 akwai Khdija daga jihar Gombe mai Million 24 akwai wata daga kano mai Million 100 akwai Bishra Idris Ummu Nasir daga Gombe mai Million 6 akwai Zaliha mai Million 18 akwai Mata da yawa wasu Million 30 wasu 40 Haka dai Mata kasaitattu a cikin zunduma zunduman Motoci suka harci zaman kotun

Mazan da suka zo kallon Shari’ar sun ta daga kai suna mamakin yadda Mata suke da manyan kudade haka Alkali ya dage zaman kotun sai – 13 – 12 – 2022 – za a dawo a cigaba da zaman kotun wannan dai shi ne abin da ya faru a takaice Allah Ya kyauta ya fitowa da mai Haqqi Haqqinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button