LABARAI/NEWS
Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Abuja Sun Kashe Wani Magidanci Da Sace ‘Ya’yansa biyu

Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Abuja Sun Kashe Wani Magidanci Da Sace ‘Ya’yansa biyu
Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun shiga yankin Ushafa da ke a anguwar Bwari a babban birnin tarayyar Abuja inda suka kashe wani Magidanci suka kuma yi awon gaba da ‘ya’yansa biyu
lamarin wanda ya afku a jiya ya faru ne da misalin karfe daya na rana wanda hakan ya jefa al’ummar yankin cikin furgici da rudani
Wata mazauniya a yankin mai suna ta ce lamarin ya afku ne a bayan wata makarantar firamare da ke yankin na Ushafa
A lokacin da ‘yan bindigar suka shigo yankin sun shafe sama da mintuna 30 suna harbi a sama ba tare da jami’an tsaro sun kawo dauki ba