Yan bindiga sun sare kan shugaban karamar hukuma a jihar imo

Yan bindiga sun sare kan shugaban karamar hukuma a jihar imo
Wasu ‘yan bindiga a jihar Imo da ke kudu maso gabashin Najeriya sun sare kan wani shugaban ƙaramar hukumar bayan da suka sace shi a ranar Juma’ar da ta gabata
Yan bindigar dai sun saki wasu hotunan bidiyo da ke nuna yadda suka ɗaure shugaban ƙaramar hukumar a hannaya da kuma yadda suka halaka shi bayan sun karɓi kuɗin fansa don su sako
rundunar yan sandan tana ƙoƙarin ceto shugaban ƙaramar hukumar daga hannun ‘yan bindigan da suka sace shi sai kwatsam a daren Lahadi aka yi aune da wasu hotunan bidiyo da ke nuna yadda aka durƙusar da shi kan gwiwoyinsa a wani ƙungurmin daji aka ɗaure masa hannaye a harɗe ta baya daga bisani kuma aka sare masa kai
Amma dai rundunar ‘yan sandan ta bayar da tabbacin tana ci gaba da gudanar da bincike har sai ta zaƙulo waɗanda ake zargi da tafka wannan aika-aika