ylliX - Online Advertising Network Yan Boko Haram 6 ne Suka baƙunci lahira a yayin wani artabu da Sojojin Nijeriya a Borno. - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yan Boko Haram 6 ne Suka baƙunci lahira a yayin wani artabu da Sojojin Nijeriya a Borno.

Yan Boko Haram 6 ne Suka baƙunci lahira a yayin wani artabu da Sojojin Nijeriya a Borno.

Dakarun bataliya ta 152 Banki na “Operation” Hadin Kai (OPHK)”, sun kashe ‘yan ta’addan Boko Haram Dakarun ”operation” hadin kai sun hallaka mutum shida ‘Yan ta’adda a Banki da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.

Wakilinmu ya tattaro cewa an kashe maharan ne a ranar Lahadin da ta gabata a wani harin kwantan ɓauna da suka yi a hanyar Kumshe zuwa Banki na kilomita.

Wani kwararre a fannin yaki da tada kayar baya kuma kwararre kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, wanda ya tabbatar da harin, ya ce dakarun sun yi kwanton bauna ne bayan wani rahoton sirri da aka samu cewa an ga wasu ‘yan ta’addan Boko Haram da dama wadanda galibi ke addabar matafiya tare da yi musu fashin kaya masu tsada.a yankin.

Ayyukan sintiri da sojojin suka yi a kan titin sun samu sakamako, inda suka kashe mutum kusan shida daga cikin ‘yan ta’addar, yayin da wasu suka tsere.

Idan dai za a iya tunawa, a ranar 11 ga watan Oktoba, sojojin na Birged 21-Armoured Brigade, Bama, Operation Hadin Kai (OPHK) sun yi nasarar kashe ‘yan ta’addan Boko Haram fiye da goma a hanyar Kumshe zuwa Banki.”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button