LABARAI/NEWS

‘Yan luwadi na daga wadanda Birtaniya za ta mayar Najeriya

‘Yan luwadi na daga wadanda Birtaniya za ta mayar Najeriya

Hukumomin Najeriya sun ce suna sa ran karbar ‘yan kasar 38 masu neman mafaka wadanda Birtaniya za ta mayar da su gida.

Mutanen sun hada da ‘yan luwadi da madigo wadanda suka nemi mafaka a Birtaniyar.

Sauran sun hada da uwaye mata da kakanni da kuma wasu mutanen wadanda suka yi shekara da shekaru a kasar.

Za su sauka a Lagos ne yau Alhamis da safe inda wani jirgi mai cike da takadama da Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Birtaniyar ta yi hayarsa zai yi jigilarsu.

Akwai kuma alamun da ke nuna cewa watakila wasu ‘yan kasar Ghana ma da za a mayar kasarsu na cikin jirgin.

Ma’aikatar harkokin waje ta Najeriya ta gaya wa BBC cewa za a mayar da mutanen gida ne saboda laifukan da suka danganci ka’idojin shige da fice.

Masu rajin kare hkkin dan-Adam a Birtaniya sun ce sun damu a kan jin dadin mutanen.

Sun ce kusan mata 10 daga cikin wadanda za a mayar na fama da tsananin cutar hauka, kuma ana ba su magani a Birtaniyar.

Masu fafutukar sun ce suna ganin idan aka mayar da mutanen kasashensu, wasu daga cikinsu za su iya fuskantar tsangwama da cin zarafi saboda addininsu ko kuma dabi’arsu ta neman jinsi daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button