FadakarwaDaga Malaman muGirki Adon Uwargida

‘Yan Mata Ga Wasu Kalaman Zuga Saurayinki Idan Ya Tambayeki Me Yasa Kike Sonsa

‘Yan Mata Ga Wasu Kalaman Zuga Saurayinki Idan Ya Tambayeki Me Yasa Kike Sonsa

Amincihausatv.com

Maza da yawa sukan nemi sanin dalilin da mace take sonsu. Da haka ne wasu mazan suke fahimtar gaskiyar Soyayyar da mace ke musu.
Ga wasu kalaman da zaki zuzuta duk wani mai sonki da aure daya tambayeki dalilinki na sonsa.

Aminci Hausa TV

1: Ki Ce Masa. “Ina sonka ne saboda kaine kai. Babu wani namiji mai irin siffarka da kyawawan halayenka”.
2: Ki sanar da shi dalilinki na sonsa, ” Nakan samu natsuwa ne a duk lokacin da nake tare dakai. Hakan yasa nake so ganin na rayu da kai har mutuwa ya raba”.
3: Furta masa cewa, “A duk lokacinda na nemi Allah Ya nuna mini mijin aurena, sai ka fado mini a rai, ko kuma na ganka a mafarkina”.
4: ” Ina sonka ne saboda yadda ka rufe kunnuwanka akan duk wasu abubuwan da aka sanar dakai game dani na gaske dana sharri”. Yi masa wannan bayanin.
5: Tabbatar masa cewa. “Daga lokacin da ka shiga rayuwata. Daga wannan lokacin na kara samun kusanci da Allah”.
6: Fahimtar da shi cewa.” Kaine ka sanar dani hakikanin yadda gaskiyan rayuwa yake. Kaine kuma ka sauya mini rayuwata”.
7: ” Kalamanka a kullum suna daurayi akan hanya madaidaici ne. Kana karfafa mini gwaiwa a dukkanin abubuwan dana saka a gaba”.
8: ” Daga ranar da na soma sonka, daga wannan ranar na soma zama cikenkiyar mace. Ta hanyar sanin yadda mace keji idan tana son namiji”.
9: ” Yanayin da mutane suke fadin alherinka, suke yabonka. Suke kara rudani a soyayyar da nake maka”.
10: Ki Jaddadamasa cewa.” Ina sonka da zuciya daya. Ina sonka tsakanina da Allah. Ina kuma fata da burin zama matarka ta har abada.

Amincihausatv.com

Ki tabbatar cewa duk namijin da zaki furta masa wadannan kalaman babu yaudara ko zolaye a ciki. Kalaman nan su fito daga birnin zuciyarki zuwa ga alkariyar tsakiyar jikin wanda kike so da kauna.
Allah Ya tabbatar mana da alheri ga fatan da muke dasu akan wadanda muke burin mu aura.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button