Fadakarwa

‘YAN MATAN ZAMANI KO ‘YAN SON ZUCIYA?

‘YAN MATAN ZAMANI KO ‘YAN SON ZUCIYA?

A duk sanda naji mata na kukan wahalar samun miji, ko aurensu na yawan mutuwa nakan girgiza kai na wuce kawai, domin kuwa hausawa na cewa” kowa ya sayi rariya yasan zata zubar da ruwa.”
Da zaka ce musu laifinsu ke janyo musu wannan matsala, da yawansu inkari zasu yi, koda yake ba duka aka taru aka zama daya ba, akwai wacce kaddara ke fadawa, akwai kuma wacce ta hadu da abokin zama bana gari ba, amma dai mafi yawa laifin daga wajen matan ne.

Duk wacce tace maka bata sami miji ba, kace da ita bata sami wanda take so ba kawai, domin Allah ya jarrabi matan wannan lokaci da son auren maikudi wanda za’a dinga buga misali a cikin kawaye, mafi yawan matan dake kokawa da rashin samun miji akwai mazan dake zuwa da niyyar aurensu wanda suke ganin kamar ba ajinsu bane, ta sanadin hakan sai mace ta kusan tsufa a gidansu babu aure, wasu Allah kan tarfawa garinsu nono su sami irin mijin da suke son aura, amma sai zaman auran ya gagara ayi ta fuskantar matsaloli saboda dama ba’a gina auren akan umarnin addini ba, watakila mijin baya iya bambance dai dai daba dai dai ba, be san hakkinki a kanshi ba, akan sami mazan da basu da lokacin matansu, akan sami wadanda basa girmama matansu sai zagi, tsawa, da hantara, wasu lokutan akan sami wanda yake fanko babu wani kudi sai karyar akwai, akan sami wanda suke da kudin amma babu zuciyar bayarwa. etc..
fada min ta yadda zaki ji dadin zaman aurea tare dashi? duk wanda kika aura domin kudi shi da kanshi ya san ba don Allah kika aure shi ba, yaudarar kanki zaki idan kikai tunanin zai zaman aure dake tsakani da Allah.

Ya ‘yar uwa shin kin mance da umarnin manzo S.A.W cewa” Idan wanda kuka yarda da dabi’un shi da halayen shi yazo neman diyarku ku aura mishi, idan ba haka fitina da barna zasu kasance a doron kasa.
ﺇﺫﺍ ﺟﺎﺀﻛﻢ ﻣﻦ ﺗﺮﺿﻮﻥ ﺩﻳﻨﻪ ﻭﺧﻠﻘﻪ ﻓﺰﻭﺟﻮﻩ، ﺇﻻ ﺗﻔﻌﻠﻮﻩ ﺗﻜﻦ ﻓﺘﻨﺔ ﻓﻲ ﺍﻷﺭﺽ ﻭﻓﺴﺎﺩ ﻛﺒﻴﺮ .” ﺭﻭﺍﻩ ﺍﻟﺘﺮﻣﺬﻱ .

Koda yake akan sami mazaje masu riko da addini amma basu da kyaun mu’amala, shi yasa Annabi S.A.W yace addini da nagarta, bai ce addini kawai ba. Yar uwa da zaki amfani da shawarar manzon tsira, ki kawar da kanki game da mai kudi, ki auri mutumin kirki mai addini, wanda yasan hakkinki a kanshi mai tausayi, inada yakinin ba zakiy dana sani ba, domin zai sauke miki duk wani hakki naki, zai girmamaki, zai kyautata miki ya faranta miki ya saki dariya, zai dinga doraki akan hanya mai kyau a nan duniya da gobe qiyama, wanda zaki sami rayuwa mai dadi tare da zuri’a mai albarka, shin akwai rayuwar data fi wannan?

Ina yawan fada cewa kudi ba shine jin dadin rayuwa ba, wani nau’in jin dadin rayuwa ne, akwai da yawan masu kudin da babu walwala ko nishadi a tare dasu. Shin me yasa da yawanku ke manta Allah ne mai azurtawa kuma shi ke talautawa, zaki iya auren maikudi ya koma talaka, zaki iya auren talaka ya koma maikudi, lamarin na Allah ne, shi abinda ake so da mutum kullum ya tsarkake zuciya ya fawwalawa Allah lamuranshi.

Kafin na rufe bari nayi tsokaci akanmu maza, muma muna da namu laifin, akwai da yawa wadanda ke raba yarinya da gidansu da danginsu su aurota zuwa gidansu su dinga zaluntarta, ba wasa da dariya, sai daure fuska da tsawa kamar wata baiwa, wasun su sukan bar matansu da garau-garau a gida a yayin da suke cin mai rai da lafiya a waje,
wannan zalunci ne. wanda hakan kan iya janyowa mutum fushin mahalicci, Manzo S.A.W na cewa” Dukkanmu an baku kiwo kuma za’a tambaye ku akan kiwon da aka baku.”
“ﻛﻠﻜﻢ ﺭﺍﻉ ﻭﻛﻠﻜﻢ ﻣﺴﺌﻮﻝ ﻋﻦ ﺭﻋﻴﺘﻪ”
Wasu ka iya cewa matan ne basa musu yadda suke so, to, wa yace kaje ka auro babbar yarinya? kaima kasan ba zata yarda ka dinga juyata yadda kake so ba, ba kowane umarni naka zata bi ba, Me yasa kaki bin umarnin Manzo S.A.W cewa” Na horeku da mata ma’abota addini da nagarta.
“ﻓﻌﻠﻴﻚ ﺑﺬﺍﺕ ﺍﻟﺪﻳﻦ ﻭﺍﻟﺨﻠﻖ”

A karshe dai ina jan hankalinmu daga mazan har matan, suyo soyayya domin Allah, ayi aure domin Allah su sani duk haduwar da babu Allah a cikinta sawa’un( Soyayya, aure, abota, kawance) wannan haduwa ba zatayi qarko ba.

Allah shi sawwaka.
Copied #Alimam

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button