ylliX - Online Advertising Network YAN MEDIA NA AREWA NUNA WARIYA, KORAFI AI BAKU GA KOMAI BA - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

YAN MEDIA NA AREWA NUNA WARIYA, KORAFI AI BAKU GA KOMAI BA

‘YAN MEDIA NA AREWA NUNA WARIYA, KORAFI AI BAKU GA KOMAI BA

‘Yan media na Arewacin Nigeria wadanda suka karbi kwangilar tallen Tinubun da bashi da farin jini a Arewa sun fara korafi sakamakon Tinubu yazo Kano, ya zauna da ‘yan Hausa film ya basu kyautar Naira Miliyan 50, amma abin takaici bai zauna da ‘yan Media na Arewa masu kareshi ba

Yanzu haka dai ‘yan Media na gidan Tinubu dake Arewa suna ta korafi a karo na biyu, bayan korafi karo na farko da sukayi lokacin da aka cire sunan ‘yan media wadanda zasu yiwa Tinubu kamfen a biyasu, sai aka zabo ‘yan alfarma wadanda basu cancanta ba akayi watsi da wadanda suka cancanta

Tabbas an fitar wa ‘yan Media na gidan Tinubu makudan kudade, ina ganin yana daga cikin dalilan da yasa aka ki hada ‘yan media na Arewa da suke kare Tinubu zama da Tinubun saboda kar asirin wadanda suka karbi kudin ya tonu

An jima ana wannan cin amanar wa ‘yan media na Arewa da suka yiwa Gwamnatin Buhari hidima, wasu azzalumai suna zuwa suna karban kudi da sunan ‘yan media na Arewa suna arzurta kansu, munyi ta Kokarin fahimtar da ‘yan media na Arewa domin su kwaci kansu amma sun gagara fahimta

Don haka baku ga komai ba, wannan abinda aka muku ana neman mulki kenan ma, ku jira ganin wulakanci da kaskanci idan wadannan mutane suka hau madafun iko wanda bama fatan Allah Ya basu nasara

Yanzu haka wata majiya daga tushe da na ji, na samu labarin Tinubu ya ware kudi kimanin Naira Biliyoyin 2 zai bawa ‘yan film, ku kam ‘yan media na Arewa wasu ne suke karban kudin da sunanku suna ta arzurta kansu

Ku yi watsi da mayaudara ‘yan jari hujja, ku dawo gidan siyasar Atiku Abubakar mu kwaci ‘yanci gaba dayan mu

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button