Yan Nigeria baku da godiyar Allah : zazzafan martanin Buhari bayan shan jifa a jihar Kano da Katsina

Shugaban Nigeria Muhammad Buhari ya bayyana cewa yan Nigeria su rings godi’ewa Allah das bin da suka samu a mulkin sa musamman managartar ayyuka da gomnatin sa tayi
Shugaban ya bayyana hakan ne a wani taro da yayi bayan ziyarar da ya kai jihar Katsina da kuma Kano inda ya bukaci yan Nigeria da su godewa Allah kan abubuwan da yayi
Wannan dai na zuwa ne a matsayin martani da shugaban yayi yan kasa Nigeria bayan da suka nuna masa Ęarara a ziyarar da kai jihohin Katsina da Kano
Haka shugaban ya kara da cewa yan Nigeria suna da mantuwa inda ya tuna musu da shekarun baya lokacin da wasu jihohin kasar nan ke hannun yan bindiga
Jihar Borno a lokacin gomnatin da ta gabata dai na hannun yan Bindiga musamman Ęanana Ęauyukan cikin jihar ta Borno inda shugaban yace sune suka kwato jihar tare da sauran guraren da yan bindiga suka kwace
Wannan magana ta shugaba kasa Muhammad Buhari dai na cigaba da shan martani hada da suka daga al ummar kasa da dama musamman la’akari da yadda kayan masarufi suke cigaba da hauhawa a kasar ta Nigeria