Yan Nigeria ku bani kwana bakwai zan magance matsalar karancin kudi cewa Buhari

A wata tattaunawa na shugaba na Nigeria yayi da mane ma labarai a fadar sa ake bila Abuja ya bukaci yan Nigeria da su bashi kwana bakwa kan ya magance matsalar karancin kudi a hannun mutane
A wani sako da shugaban kasa Buhari ya fita a birnin tarayyar Abuja ya bukaci yan Nigeria da su bashi kwana bakwai domin magance matsalar dake addabar al ummar kasa ta rashin kuɗi a hannun su
Wannan a zuwa ne bayan da al umma kasar ke cigaba da kokawa kan karancin kudi a hannun su tun bayan da babban bankin kasa CBN ya sauya fasalin kudin na Naira
Buhari dai na cigaba da fuskantar kalubale musamman bayan chanza fasalin kudi da yayi a wanna shekara da muke ciki lamarin da ya haifar da takura da kuma jefa al umma kasa cikin tsaka mai wuya
Al umma kasar Nan dai na kallon chanzin kudi a matsayin wata hanya ta gallazawa talakawa tun da cewa chanzin na da matuƙar alfanu musamman lokacin zabe wanda yan siyasa ke amfani da kudin da suka sake wajen rabawa talakawa don su zabe su