ylliX - Online Advertising Network Yan sanda sun cafke wadanda, suka sace yaro nan, Fadil Aliyu, a Barassa Hotal dake Mubi - AMINCI HAUSA TV
LABARAI/NEWS

Yan sanda sun cafke wadanda, suka sace yaro nan, Fadil Aliyu, a Barassa Hotal dake Mubi

Yan sanda sun cafke wadanda, suka sace yaro nan, Fadil Aliyu, a Barassa Hotal dake Mubi

Rundunar ‘yan sandan da ke aiki a ofishin hukumar leken asiri ta jihar (SIB) a jihar Adamawa ta samu nasarar cafke wasu miyagu da suka sace yaron nan fadil Aliyu Mustapha wanda aka yayata Hotunansa, a Facebook, duk kuwa da sun biya kudin fansa miliyan Hudu, da Dubu Saba’in da Tara, a matsayin kudin fansa, kamar yadda SP suleiman Yahaya Nguruje ya shai dawa Yola 24

Yan sanda sun samu rahoto game da sace yaron mai suna Mustapha Aliyu Fadil dan shekara 8 a karamar hukumar Mubi, an gano yaron a Barassa Hotel da ke Mararraban Mubi.

Bayan samun rahoton, rundunar ta yi gaggawar tsara wata dabarar da hukumar leƙen asiri ta jagoranta kuma ta yi sa’a ta kama waɗanda ake zargi kamar haka:-

(1) Zaiyat Adamu mai shekaru 19, mazauniyar Tashan Gella, karamar hukumar Mubi ta Kudu.

(2) Abdulrahman Abubakar dan shekara 31, mazaunin Shagari Low-cost, karamar hukumar Mubi ta Arewa

(3) Haruna Yakubu dan shekara 21, mazaunin unguwar Kaban, karamar hukumar Mubi ta Arewa.

(4) Abubakar Muhammed, dan shekara 20, mazaunin Angwan Ba-talaka, karamar hukumar Mubi ta Arewa.

(5) Isa Musa dan shekara 21, mazaunin Angwan Ba-talaka Mubi North, karamar hukumar.

Wadanda ake zargin sun hada baki ne tare da lallasa wand aka tsare shi tsawon kwana biyu sai da aka biya su kudin fansa miliyan biyar kamar yadda suka nema kafin su sako wanda aka sacen

Kwamishinan ‘yan sanda
CP SK Akande ya yaba wa sashin binciken manyan laifuka ta SIB da mutanensa kan irin na mijin kokarin da suka yi, ya umurci Jami’ai da Maza da su ci gaba da aiki a matsayin dabarun binciken laifuka da masu aikata laifuka a cikin jihar da kewaye.

Kwamishinan ya yi kira ga al’umma da su rika sanar da ‘yan sanda duk inda suka kalla masu aikata laifuka da maboyarsu, musamman wadanda ake kokwanto akan su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button